News
An Bukaci Iyaye Su Kara Sa Ido Kan ’Ya’yansu A Lokacin Ramadana
An bukaci iyaye da su kara kula da mu’amalar ’ya’yansu domin kare su daga fadawa munanan dabi’u, musamman a wannan lokaci na watan Ramadan.
Kiran ya fito ne daga Comrade Nasiru Alhassan Dambatta, daya daga cikin ’yan kwamitin inganta dangantaka tsakanin jami’an tsaro da al’umma, yayin da yake tsokaci kan matakan da hukumomi suka dauka na hana wasu ayyukan da ka iya tayar da hankali a cikin al’umma.
Iran Tayi Watsi Da Ikirarin Shiga Tattaunawa Da Amurka
Ya ce matakin da Rundunar ’Yan Sanda Najeriya da Hukumar Hisbah suka dauka na haramta gudanar da wasan Tashe a watan Ramadan na da nufin tabbatar da zaman lafiya da tsaro.
A cewarsa, ya zama wajibi kwamitin PCRC ya ci gaba da sanya ido domin tabbatar da bin dokar yadda ya kamata a fadin yankin.
Har ila yau, ya yi kira ga kungiyoyin sa kai da na cigaban al’umma da su dauki matakan dakile abin da ya kira mummunar dabi’ar “buga knockout,” musamman a lokutan buda baki, yana mai cewa al’ada ce marar amfani wadda ka iya janyo rikici da barazana ga zaman lafiya.
Comrade Nasiru ya kuma yabawa shugabannin karamar hukumar Dambatta da jami’an tsaro da sarakunan gargajiya bisa kokarin da suke yi wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin, tare da kira ga al’umma da su ci gaba da ba su hadin kai domin dorewar tsaro da kwanciyar hankali.
-
News1 day ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News2 days ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
