News
Iran Tayi Watsi Da Ikirarin Shiga Tattaunawa Da Amurka
Jamhuriya muslunci ta Iran ta yi watsi da ikirarin shugaban Amurka Donald Trump kan cewa ta bukaci a tattauna duk da hare-haren da su ke cigaba da kaiwa juna.
Yayin da aka Shiga ƙwana na uku a jere da faro yakin, ma’aikatar tsaron Amruka Pentagon ta ce dakarun kasar uku sun gamu da ajalinsu wasu biyar kuma sun samu munanan raunuka a hare-haren makami mai linzami da Iran ta kai kan sansaninta na Centcom a Gabas ta Tsakiya.
Mun Gano Na’urorin Sauraren Sirrin Mutane a Gidan El-Rufai – ICPC
A nata bangare rundunar sojin Isra’ila ta ce ta yi nasara hallaka manyan kwamandojin sojin Iran akalla 40 da suka hada da ministan cikin gida da shugaban rundunar dakarun juyin juya halin ƙasar ba yaga jagoran addini muslunci AyatollAh Ali Khamenei da shi ma ya rasa ransa a farmakin.
A matsayin martani, dakarun rundunar kundun bala Kasar Iran IGRC ta harba makamai masu linzami a sassan Biranen Tel aviv da Jérusalem da ma wasu sansanonin sojin Amruka da ke Gabas ta Tsakiya.
Ƙungiyar agaji ta Red Cross ta shaida mutuwar mutum 9 yayin da wasu 11 suka ɓata sakamakon a lardin Bet Shemesh na Isra’ila sakamakon hare-haren Iran.
Haka ma jaridu a yankin sun ruwaito cewa akalla mutum hudu sun mutu yayin da wasu 58 suka jikkata bayan da Iran tayi ruwan makamai masu linzami kan biranen Doha,da Bahreïn da kuma Oman.
-
News1 day ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News2 days ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
