Connect with us

News

Wani Jirgin Yakin Sojin Sama Ya Yi Hatsari A Neja

Published

on

NAF 2 How fighter jet
Spread the love

Wani jirgin yaki na rundunar Sojin Saman Najeriya (NAF) ya yi hatsari a sansanin rundunar da ke Kainji, Jihar Neja, bayan samun matsalar gaggawa jim kaɗan da tashinsa. Duk da haka, matuƙan biyu sun tsira bayan yin “ejection” cikin kwarewa.

A wata sanarwa da mai magana da yawun NAF, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya fitar ranar Asabar, ya ce jirgin nau’in Alpha Jet yana kan gwajin aiki ne bayan kammala gyara kafin ya sami matsalar fashewa.

Jami’an Kwastam Sun Kama Wani Jirgin Ruwan Brazil Ɗauke Da Hodar Iblis A  Lagos

Ejodame ya ce matuƙan sun karkatar da jirgin daga yankunan da ake zaune kafin su yi tsalle domin kare rayukan fararen hula. Ya kuma tabbatar da cewa an mika su cibiyar lafiya ta NAF domin binciken lafiyar su cikin gaggawa.

 

 

THE NATION

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *