Connect with us

News

Jami’an Ƴansanda Sun Kama Ƴan Fashin Daji Da Ke Kai Hare-hare Da Garkuwa Da Mutane A Wasu Jihohin Arewacin Najeriya

Published

on

Kwara Bandit
Spread the love

Rundunar ƴansandan Nijeriya ta ce ta kama wasu mutane biyu da ake zargi mambobin ƙungiyar ƴan fashin daji ne da ke kai hare-hare da garkuwa da mutane a wasu jihohin arewacin ƙasar.

An kama mutanen ne a ranar 19 ga Disamba a yankin Komen–Masallaci, da ke ƙaramar hukumar Kaiama a jihar Kwara, a cewar rundunar.

Kotun Ghana Ta Daure ‘Yar Najeriya Watanni 15 Kan Cin Zarafin ‘Yarta ‘Yar Shekara 9

Ɗaya daga cikin waɗanda aka kama shi ne Abubakar Usman, wanda aka fi sani da Siddi, wanda aka gani a wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta yana rike da makamai da kuɗaɗe. Na biyun kuma shi ne Shehu Mohammadu, wanda ake kira Gide.

Ƴansandan sun ce a yayin samamen sun kwato babur Honda Ace 125, kuɗi naira 500,000, da bindigar AK-47 tare da harsasai guda 20.

A cewar jami’an tsaro, binciken farko ya nuna cewa mutanen na da alaƙa da wata ƙungiyar ƴan fashin daji da ke aiki a jihohin Katsina, Zamfara, Neja da Kwara, tare da zargin cewa suna shiga harkokin samar da makamai.

Rundunar ta ce waɗanda ake zargin suna ba da haɗin kai ga masu bincike, yayin da ta bukaci jama’a da su ci gaba da bayar da sahihan bayanai domin taimakawa ayyukan tsaro.

 

 

Channels TV 

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *