Connect with us

News

Jami’an ’Yan Sanda Sun Tabbatar Da Fashewar Bam A Zamfara

Published

on

1766869279793
Spread the love

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara, ta tabbatar da fashewar bam a hanyar Dansadau zuwa Magami, lamarin da ya yi sanadin mutuwar wasu matafiya.

Kakakin rundunar, DSP Yazid Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa.

An Hallaka Wani Matashi Saboda Cajar Waya A Anambra

“Rundunar ’Yan Sanda ta karɓi rahoton wani mummunan lamari da ya faru a yau, 27 ga watan Disamba, 2025, da misalin ƙarfe 2:30 na rana, a kan hanyar Magami–Dansadau, a ƙauyen Maikogo da ke Ƙaramar Hukumar Maru.”

Advertisement

 

DSP Yazid Abubakar ya ce rahoton ya isa hedikwatar rundunar ne ta hannun Jami’in ’Yan Sanda mai kula da sashen Magami.

“Bayanin da aka samu daga Jami’in da ke kula da ofishin Magami (OC) ya nuna cewa wani abu da ake zargin bam ne, wanda da ba a san ko su waye ba suka dasa, ya fashe a wajen.”

Advertisement

Sanarwar ta ƙara da cewa fashewar ta lalata wata mota, tare da hallaka wasu mutane ciki har da wani babur da ke kusa da wajen lokacin da lamarin ya faru.

“A halin yanzu, adadin waɗanda abin ya shafa bai bayyana ba. Sai dai an tura jami’an tsaro zuwa wajen.

“Ana ci gaba da bincike domin tantance yawan asarar rayuka tare da tabbatar da tsaron yankin don kauce wa wani hatsarim.”

Advertisement

Kakakin ya ƙara da cewa rundunar ta fara bincike kan musabbabin lamarin, yayin da ƙwararru da sauran sassan da abin ya shafa ke wajen domin tantance halin da ake ciki.

Rundunar ta yi kira ga al’umma da su kasance cikin natsuwa, su yi taka-tsantsan, tare da kai rahoton duk wani abun zargi zuwa ofishin ’yan sanda mafi kusa ko wata hukuma ta tsaro.

“Za mu ci gaba da sanar da jama’a duk wani sabon bayani da muka samu,” in ji DSP Yazid.

Advertisement

 

 

AMINIYA

Advertisement
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *