News
Fadar Sarkin Musulmi ta sanar da cewa an ga watan Azumin Ramadan a Najeriya
Fadar Sarkin Musulmi ta bayyana cewa an ga jinjirin watan Azumin Ramadan a na shekarar Musulunci ta 1447, a Najeriya.
Cikin wata sanarwa da fatar Sarkin Musulumin ya fitar a ranar Talata da daddare, ya ce an samu bayanan ganin watan a wurare daban-daban a ƙasa.
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 10 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Katsina
Kafar BBC Hausa ta ruwaito cewa, fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi, ta umarci Musulman Najeriya, su fara azumin Watan Ramadan a ranar Laraba 18 ga watan Fabrairun 2026.
Matakin na alamta shigar watan Ramadan mai alfarma – wanda musulmi a faɗin duniya ke gudnar da ibadar azumi, ɗaya daga cikin shika-shikan musulunci biyar.
