Connect with us

News

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 10 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Katsina

Published

on

‎Burkina Faso ta saki sojojin Najeriya Da Take Rike Da Su Na Tsawon Kwanaki 10

Dakarun Operation FANSAN YANMA tare da haɗin gwiwar sauran jami’an tsaro sun kuɓutar da mutum 10 da aka sace a ƙauyen Madakin Hurya da ke ƙaramar hukumar Kankara dake jihar Katsina

Rahotanni sun ce ‘yan bindiga sun kai farmaki ƙauyen da misalin ƙarfe 11 na dare a ranar 16 ga Fabrairu, inda suka sace mutane da dama tare da kwashe tumaki 30.

Advertisement

Gwamnatin Kano Ta Kaddamar Da Rigakafin Shanu Miliyan 1.5 Don Dakile Cutar CBPP ‎

Jami’an tsaro sun bi sahun maharan, kuma bayan musayar wuta mai tsanani, ‘yan bindigar sun tsere zuwa daji da raunukan harbi. Dukkan mutanen da aka sace an kuɓutar da su ba tare da rauni ba, sannan an mayar da dabbobin da aka kwato ga mazauna yankin.

Advertisement

Hukumomi sun ce an dawo da zaman lafiya, yayin da ake ci gaba da farautar maharan da suka tsere.

 

Advertisement

PRNIGERIA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending