Connect with us

News

Kamfanin Maltina Ya Ƙaddamar da Shirin Bunƙasa Noman Sha’ir a Jigawa, Manoma 20,000 Za Su Amfana

Published

on

IMG 20260306 WA0062

Kamfanin Maltina ya bayyana cewa zai samar da ayyukan yi ga manoma sama da 20,000 a Jihar Jigawa nan da shekarar 2030, a wani sabon shiri da kamfanin ya ƙaddamar domin bunƙasa noman sha’ir (barley) da kuma ƙarfafa tattalin arzikin al’umma.

IMG 20260306 094712 045

‎Shirin, wanda aka gabatar da taken “Scaling Local Barley and Empowering Communities,” na da nufin tallafa wa manoma su rungumi noman zamani, tare da rage dogaro da shigo da irin sha’ir daga ƙasashen waje.

Advertisement

IMG 20260306 104824 649

‎Daraktan sashen Supply Chain na kamfanin, Federico Agressi, ya ce kamfanin ya ƙaddamar da shirin ne domin ƙarfafa manoma su koma yin noman zamani wanda zai ƙara yawan amfanin gona da kuma bunƙasa tattalin arzikin al’ummomin karkara.

‎Ya ce a halin yanzu Najeriya na shigo da tan dubu 200 na sha’ir a kowace shekara, lamarin da ke sa a kashe kimanin dala miliyan 150 wajen shigo da irin daga ƙasashen waje.

Advertisement

images (5)

‎A cewarsa, burin shirin shi ne a samar da wannan amfanin gona a cikin gida, ta yadda za a rage kuɗaɗen da ake kashewa wajen shigo da shi daga waje, tare da samar da ci gaba mai ɗorewa ga manoma.

IMG 20260306 104111 953

‎A nasa jawabin, Manajan Daraktan kamfanin, Tibo Brochain, ya ce shirin yana daga cikin ƙoƙarin kamfanin na samar da ayyukan yi da kuma bunƙasa harkar noma a Najeriya.

Advertisement

‎Ya ce an fara aiwatar da shirin a jihohi da dama da suka haɗa da Bauchi, Kano, Plateau, Gombe, Yobe da Jigawa, domin tallafa wa manoma da kuma ƙarfafa samar d sha’ir a cikin gida.

IMG 20260306 100819 372

‎Brochain ya kuma gode wa cibiyoyin bincike, kamfanoni masu zaman kansu da hukumomin gwamnati da suka ba da goyon baya wajen ganin shirin ya samu nasara.

Advertisement

IMG 20260306 111320 623

‎Shi ma Dutel Ambassador, Bengt Van-L, ya ce shirin na da burin sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da za su zama kan gaba wajen noman sha’ir idan aka ci gaba da irin wannan haɗin gwiwa tsakanin manoma da kamfanoni masu zaman kansu.

IMG 20260306 115237 388

‎Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, wanda Kwamishinan Noma na jihar, Muttaka Namadi, ya wakilta, ya ce shirin babbar dama ce ga jihar da ta shahara wajen harkar noma.

Advertisement

‎Ya ce gwamnatin jihar na maraba da wannan shiri saboda zai taimaka wajen ƙara samar da ayyukan yi, bunƙasa tattalin arzikin manoma da kuma ƙara yawan amfanin gona.

images (5)

‎Haka kuma ya yaba wa kamfanin Maltina kan wannan shiri, yana mai cewa manoma a jihar sun nuna farin ciki da yadda shirin zai ƙara musu hanyoyin samun kuɗaɗen shiga.

Advertisement

IMG 20260306 113123 515

‎A nasa jawabin, Sarkin Ringim, Alhaji Sayyadi Abubakar Mahmoud (CON) wanda Madakin Ringim, Alhaji Bashir Sha’aibu, ya wakilta, ya yi kira ga manoma su ba kamfanin cikakken haɗin kai domin tabbatar da nasarar shirin.

IMG 20260306 114135 316

‎Shi kuma Shugaban manoman Ringim, Dr. Mujitapha Ubaye, ya ce manoma sun shirya tsaf domin yin iya ƙoƙarinsu wajen samar da amfanin sha’ir fiye da yadda aka tsara.

Advertisement

IMG 20260306 113859 116 IMG 20260306 095641 088 IMG 20260306 103956 083 IMG 20260306 112145 632IMG 20260306 093952 281

‎Taron ƙaddamar da shirin ya samu halartar wakilan cibiyoyin binciken noma, hukumomin gwamnati da kuma manyan baƙi daga sassa daban-daban na Najeriya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending