Connect with us

News

Gwamnatin Kano Ta Nuna Damuwa Kan Karancin Komawar Dalibai Makarantu Bayan Kammala Hutun Sallah

Published

on

Makaranta
Advertisements
Advertisements
Spread the love

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana damuwa matuƙa kan yadda ɗalibai da dama ba su koma makarantu ba bayan kammala hutun Sallah ƙarama.

Babban Sakataren Ma’aikatar Ilimi ta jihar, Alhaji Bashir Baffa Muhammad, ne ya bayyana hakan a wata hira da kafar Arewa Radio, bayan da ya gudanar da rangadi domin duba halin komawar ɗalibai a wasu makarantun gwamnati.

Jami’an Hisbah Sun kama mata sama da 280 Da Su Ka Yi Shigar Banza A Bukukuwan Sallah A Kano

Advertisement

Ya ce ya ziyarci makarantu sama da 15 a faɗin jihar, inda ya tarar da ƙarancin halartar ɗalibai duk da cewa an buɗe makarantu a hukumance domin ci gaba da karatu.

A cewarsa, halin da aka tarar abin takaici ne, la’akari da yadda aka sanar da ranar komawa makaranta tun kafin ƙarshen hutun.

Gwamnatin ta yi gargaɗin cewa ba za ta lamunci ci gaba da irin wannan hali ba, tana mai cewa za ta ɗauki matakan da suka dace domin magance matsalar.

Advertisement

Haka kuma, ta yi kira ga iyaye da masu kula da yara da su tabbatar da cewa ‘ya’yansu sun koma makaranta cikin gaggawa, tare da jaddada muhimmancin ilimi ga ci gaban al’umma.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending