News
NDLEA Ta Nuna Damuwa Kan Ƙarancin Jami’an Mata A Kano
Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (National Drug Law Enforcement Agency – NDLEA) a jihar Kano State ta bayyana damuwa kan ƙarancin jami’an mata a rundunar, tana mai cewa hakan na kawo cikas ga gudanar da wasu muhimman ayyukanta.
Kwamandan hukumar a jihar, D.Y. Lawal, ya bayyana hakan ne a yayin wani taron tattaunawa da aka gudanar a birnin Kano domin bikin International Women’s Day.
Jami’an Hisbah Sun Kama Matasa Kusan 300 Da Suka Yi Askin Banza Da Kuma Kitso A Kano
A cewarsa, ƙarancin jami’an mata na shafar yadda hukumar ke tafiyar da ayyuka musamman waɗanda suka shafi bincike da kula da shari’o’in da suka danganci mata.
Ya ƙara da cewa, ƙara yawan mata a cikin hukumar zai taimaka wajen inganta aiki da kuma ƙarfafa ikon ta wajen magance matsalolin da suka shafi jinsi.
Har ila yau, ya nuna damuwa kan yadda ake samun ƙaruwar mata da ke shiga harkar ta’ammali da miyagun ƙwayoyi a jihar, yana mai cewa hakan na buƙatar ɗaukar matakan gaggawa.
Taron ya haɗa mahalarta daga ƙungiyoyi daban-daban, inda aka tattauna batutuwan da suka shafi haƙƙin mata, adalci da kuma daidaito a cikin al’umma.
