News
Abin Mamaki: Garin Utqiagvik Na Alaska Inda Rana Ke Haskawa Har Kwana 84 Ba Tare Da Faɗuwa Ba
Wani abin al’ajabi na yanayi na ci gaba da jan hankalin duniya a garin Utqiagvik da ke arewacin jihar Alaska, inda rana ke ci gaba da haskawa ba tare da faɗuwa ba har tsawon kwanaki 84.
Garin, wanda ake kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin wuraren da suka fi kusa da yankin Arctic Circle, na fuskantar abin da masana ke kira Midnight Sun, wato yanayin da rana ba ta ɓuya gaba ɗaya saboda karkatar da duniya ke yi yayin zagayowarta.
Dan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar PDP Amb. Muhammad Bello Dalha ya Matar Da Form Din Takararsa
Rahotanni sun nuna cewa daga tsakiyar watan Mayu zuwa farkon watan Agusta, mazauna garin na rayuwa cikin hasken rana na awanni 24 a kullum, lamarin da ke sa dare ya zama tamkar rana.
Masana sun bayyana cewa wannan yanayi na faruwa ne saboda matsayin yankin a doron ƙasa, inda rana ke ci gaba da bayyana sama ba tare da sauka a gindin sararin samaniya ba.
Duk da cewa lamarin na ɗaukar hankalin masu yawon buɗe ido daga sassa daban-daban na duniya, wasu mazauna yankin sun bayyana cewa rashin dare na iya sauya yanayin barci da tsarin rayuwar mutane.
Sai dai duk da haka, garin Utqiagvik ya zama ɗaya daga cikin wuraren duniya da ake yawan ziyarta domin shaida wannan abin mamaki na halitta, wanda ke nuna irin ikon da Allah yayi awannan yankin.
-
News1 day ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News2 days ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
