Connect with us

News

Fiye Da Mutane 100 Sun Mutu A Harin Dakarun Sojin Sama Da Aka Kai Kasuwa A Zamfara

Published

on

Wani Jirgin Rundunar Sojin Saman Najeriya Ya Hallaka Mutane Da Dama A Sokoto 

Wani harin sama da sojoji suka kai kan kasuwar Tumfa da ke ƙaramar hukumar Zurmi a Jihar Zamfara ya yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutane 117 tare da jikkata wasu da dama. Mazauna yankin sun ce waɗanda suka mutu sun haɗa da ‘yan bindiga da mutanen yankin. In ji rahoton Daily Trust

‎An kai harin ne a ranar Lahadi, ranar da rundunar kuma ta kai makamancin wannan harin a Guradnayi, kusa da Kusasu a ƙaramar hukumar Shiroro ta Jihar Neja, inda ya kuma yi sanadiyyar mutuwar mutane mazauna yankin su 13.

Advertisement

Abin Mamaki: Garin Utqiagvik Na Alaska Inda Rana Ke Haskawa Har Kwana 84 Ba Tare Da Faɗuwa Ba ‎

‎Rahotannin harin da aka kai Tumfa sun bayyana ne a ƙarshen ranar Litinin saboda matsalar sadarwa a yankin.

Advertisement

‎An ce Tumfa da wasu ƙauyukan da ke maƙwabtaka da ita a ƙaramar hukumar Zurmi na ƙarƙashin ikon ‘yan bindiga, inda mazauna yankin ke rayuwa tare da su saboda su ne suke da iko da yankin kamar hukumomin gwamnati.

‎Wani jagoran al’umma, Garba Ibrahim Mashema, ya ce har yanzu yana da wahala a tantance ainihin yawan waɗanda suka mutu a harin saman da aka kai kasuwar ranar Lahadi.

Advertisement

‎“A yanzu yana da wahala a tantance cikakken adadin waɗanda suka mutu. Kowa — mazauna gari da ‘yan bindiga — na zuwa kasuwar. Jama’a na rayuwa ne ƙarƙashin ikon ‘yan bindiga, babu abin da za su iya yi,” in ji shi yayin tattaunawa da AFP.

‎Aliyu Musa, wani mazaunin garin Zurmi da ke kimanin kilomita bakwai daga Tumfa, ya ce da dama daga cikin waɗanda suka mutu ‘yan kasuwa ne da masu sayar da abinci, ciki har da ‘yan mata masu sayar da kunu da awara. Ya kiyasta yawan mace-macen zuwa 117.

Advertisement

‎“Gaskiya ne, kasuwar Tumfa na ƙarƙashin ikon ‘yan bindiga. Ita ce sansaninsu. Duk wanda ya je can ya san ya shiga yankinsu,” in ji Musa.

‎Wani ɗan uwan wasu daga cikin waɗanda abin ya shafa, wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilan tsaro, ya ce jirgin yaƙin sojoji ya fara shawagi a saman kasuwar domin bincike kafin ya dawo bayan wasu sa’o’i ya kai harin bam.

Advertisement

‎Ya kuma ce wasu ƙauyuka a ƙaramar hukumar kamar Fakai, Mayasa da Mashema na ƙarƙashin ikon ‘yan bindiga saboda babu wata hukuma ta gwamnati a yankunan.

‎“Babu wata hukuma ta doka a ƙauyuka kamar Fakai, Mayasa da Mashema. ‘Yan bindiga ne suka zama alkalai da ‘yansanda,” in ji shi.

Advertisement

 

LEADERSHIP

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending