News
Rikicin ADC: Naja’atu Ta Zargi Sheikh Ibrahim Khalil Da Mara Wa Tinubu Baya
Mataimakiyar Shugaban Jam’iyyar ADC ta ƙasa mai kula da shiyyar Arewa maso Yamma, Hajiya Naja’atu Muhammad, ta zargi ɗaya daga cikin masu neman takarar gwamnan Kano a jam’iyyar, Sheikh Ibrahim Khalil, da nuna goyon baya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu fiye da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar.
Naja’atu ta yi wannan zargin ne yayin da take magana da manema labarai, inda ta ce kwamitin sasanci da tantance ‘yan takara na jam’iyyar bai amince a bai wa Sheikh Ibrahim Khalil tikitin takarar gwamna ba.
A cewarta, dalilin hakan shi ne abin da ta bayyana a matsayin rashin cikakken goyon bayan Sheikh Ibrahim Khalil ga jam’iyyar da kuma ɗan takararta na shugaban ƙasa.
Ta kuma yi ikirarin cewa kalamai da matsayin Sheikh Ibrahim Khalil kan harkokin siyasa sun nuna cewa ya fi yabawa da goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu fiye da Atiku Abubakar, duk da cewa Atiku ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar.
Wannan na zuwa ne a lokacin da ake ci gaba da fuskantar rikici a jam’iyyar ADC reshen Jihar Kano, inda tsagin da Hajiya Naja’atu Muhammad ke jagoranta ya tsayar da Ibrahim Ali Amin, wanda aka fi sani da Little, a matsayin ɗan takarar gwamna, yayin da wani tsagin jam’iyyar ya tsayar da Sheikh Ibrahim Khalil.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Sheikh Ibrahim Khalil bai fito fili ya mayar da martani kan zarge-zargen da Hajiya Naja’atu Muhammad ta yi masa ba.
-
News4 days ago
Hukumar Kula Da Harkokin Shari’a Ta Tilasta Wa Alƙali Ritaya Kan Zargin Karɓar Cin Hancin Naira 250,000 A Kano
-
News5 days ago
Jigawa: Sama da Gine-gine 200 Sun Lalace Sakamakon Iska Da Ruwan Sama Mai Ƙarfi
-
News4 days ago
Wasu Fusatattun Matasa Sun Hallaka Wani Mutum Tare Da Kona Gawarsa Kan Zargin Satar Babur A Kano
