News
Kotu Ta Yanke Wa Tsohon Jami’in Gwamnatin China Hukuncin Kisa Kan Badakalar Cin Hanci
Wata kotu a China ta yanke wa tsohon jami’in gwamnatin kasar Yang Youlin hukuncin kisa bayan samun sa da laifin karɓar cin hanci da ya kai fiye da yuan biliyan 2.2, kwatankwacin dala miliyan 325, a cikin shekaru kusan 30 da ya yi yana riƙe da mukaman gwamnati.
Yang ya yi aiki a muƙamai daban-daban a birnin Nanjing tsakanin shekarun 1993 zuwa 2023, ciki har da mataimakin daraktan yankin bunƙasa tattalin arziki da fasaha na Nanjing da kuma shugaban wasu hukumomin raya yankin.
ICPC Ta Kama Likitan El-rufai Bayan Ganawa Da Shi
A hukuncin da kotun ta yanke ranar Litinin, an kuma same shi da laifukan almundahanar kuɗaɗen gwamnati, karkatar da kadarorin jama’a, amfani da iko ba bisa ka’ida ba da kuma safarar kuɗaɗen haram.
Kotun ta bayyana cewa Yang ya yi amfani da matsayin sa wajen karkatar da kwangilolin gine-gine, mu’amalolin kasuwanci, canja wurin filaye da harkokin kuɗi domin samun kadarori da kuɗaɗe da darajarsu ta kai yuan biliyan 2.214, lamarin da ya sanya shari’ar sa cikin manyan shari’un cin hanci da aka taɓa yi a China.
Binciken ya kuma gano cewa tsakanin 2014 da 2016, ya haɗa baki da wasu mutane wajen wawure yuan miliyan 12 daga asusun gwamnati.
Haka kuma ya biya wasu jami’an gwamnati cin hanci da ya haura yuan miliyan 25 domin samun wasu biyan bukata ba bisa ka’ida ba.
