News
Kotu Ta Hana Wani Babban Jami’in Gwamnati Zuwa Aiki Hajji
Babbar Kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta yi watsi da buƙatar da Akanta Janar na jihar Bauchi, Sirajo Muhammad Jaja, ya gabatar na neman izinin fita zuwa kasar Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin bana.
Akanta Janar din na fuskantar tuhuma kan zargin hannu a badakalar kuɗaɗen gwamnati da suka haura naira miliyan dubu ɗaya da miliyan 600, zargin da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC ke yi masa tare da wasu mutane.
Fiye Da Mutane 100 Sun Mutu A Harin Dakarun Sojin Sama Da Aka Kai Kasuwa A Zamfara
Yayin yanke hukuncin, Mai shari’a Obiora Egwuatu ya bayyana cewa kotun ba ta gamsu da dalilan da aka gabatar wajen neman wannan izini ba, musamman duba da yadda shari’ar ke gaban kotu kuma ake ci gaba da sauraren ta.
Kotun ta ce ba za ta bayar da damar da ka iya kawo tsaiko ko tangarɗa a shari’ar ba, sannan ta ɗage ci gaba da sauraron ƙarar zuwa ranar 30 ga watan Yunin shekarar 2026.
Lauyoyin masu gabatar da ƙara sun yi maraba da matakin kotun, yayin da ake sa ran bangarorin shari’ar za su sake bayyana a gaban kotun a ranar da aka sanya domin ci gaba da shari’ar.
