News
An Dakatar Da Shige Da Ficen Motoci A Bello Road Kasuwar Singa Daga Karfe 5 Na Yamma Zuwa 7 Na Safiyar Kowacce Rana
An dakatar da shige da fice na manyan motoci, matsakaita da ƙananan motoci a yankin Bello Road da Kasuwar Singa da ke Kano, daga ƙarfe 5:00 na yamma zuwa 7:00 na safiya kowace rana.
Matakin ya biyo bayan ayyukan gyaran tituna da gwamnatin Jihar Kano ke gudanarwa a yankin, domin ba da damar gudanar da ayyukan cikin sauƙi da kuma rage cunkoson ababen hawa.
Allah Ya Yi Wa Kakakin Hukumar Kashe Gobara Ta Jihar Kano, CFO Saminu Yusuf Abdullahi, Rasuwa
Sai dai, ƴan kasuwar da ke saye ko sauke kaya a cikin kasuwar za su iya ci gaba da ayyukansu daga ƙarfe 6:00 na safe zuwa 5:00 na yamma kowace rana.
Shugaban Ƙungiyar Ci gaban Kasuwar Singa (SIMDA), Barista Junaidu Zakari Muhammad, ne ya bayyana hakan a wani saƙon murya da ya aika wa Arewa Radio.
Ya ce an ɗauki matakin takaita zirga-zirgar ne domin bai wa ma’aikatan da ke aikin gyaran titin damar gudanar da ayyukansu cikin nutsuwa, tare da rage wahalhalun da ƴan kasuwa da masu amfani da titin ke fuskanta sakamakon cunkoso.
Barista Junaidu ya kuma yabawa gwamnatin Jihar Kano kan ayyukan gyaran tituna da gina magudanan ruwa da take gudanarwa a Kasuwar Singa.
Ya ce ayyukan za su taimaka wajen inganta yanayin kasuwar da kuma samar da ingantaccen tsarin kasuwanci na zamani.
