Connect with us

News

An Kama Wani Matashi Da Ya Je Zana Wa Mahaifinshi Mai Shekaru 67 Jarrabawar Ƙarin Girma

Published

on

IMG 4353

An kama wani matashi mai shekaru 33, Monsuru Musa, bisa zargin rubuta jarrabawar ƙarin girman aikin gwamnati a madadin mahaifinsa, Musa Mohammed.

Musa Mohammed ma’aikaci ne a Hukumar Kashe Gobara ta Babban Birnin Tarayya (FCT), kuma ana zargin ɗansa ya yi kwaikwayonsa ne a lokacin jarrabawar da ake gudanarwa domin ƙarin girma ga ma’aikatan gwamnatin Abuja

Kwamishinan Ƴansandan Kano Ya Bukaci Sarki Aminu Ado Ya Janye Shirin Sa Na Hawan Fatahu Yakasai 

An kama Monsuru ne a ranar Laraba, wato rana ta uku ta jarrabawar, a cibiyar jarrabawar da ke harabar Jami’ar  NOUN da ke Abuja.

Rahotanni sun ce an tsaurara matakan tsaro a cibiyoyin jarrabawar ne domin dakile maguɗin jarrabawa da kuma hana masu kwaikwayo shiga rubuta jarrabawar a madadin wasu.

A lokacin da ake yi masa tambayoyi, Monsuru ya ce mahaifinsa ba shi da lafiya, shi ya sa ya turo shi domin ya rubuta jarrabawar a madadinsa.

Advertisement

Sai dai ya kuma ce mahaifinsa yana cikin harabar NOUN, duk da cewa rashin lafiyar tasa ta hana shi rubuta jarrabawar da kansa.

Lamarin ya ƙara rikicewa bayan jami’an tsaro sun tambayi Monsuru shekarun mahaifinsa, inda ya ce mahaifin nasa yana da shekaru tsakanin 67 zuwa 68.

Sai dai Musa Mohammed ya bayar da wani bayani dabam, inda ya ce zai cika shekaru 60 a watan Fabrairun 2027.

Binciken farko ya kuma nuna cewa Musa ya kammala makarantar firamare a shekarar 1977, sannan ya kammala sakandare a shekarar 1982.

Bayan an yi musu tambayoyi, an miƙa mahaifin da ɗansa ga ’yan sanda domin ci gaba da bincike, bayan da suka bayar da bayanai ga jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS).

 

Advertisement

 

THE SUN 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending