Connect with us

News

Wani Yaro Mai Shekara 9 Ya Ƙona Gidan Mahaifinsa Bayan An Zarge Shi Da Satar Kaza A Yobe

Published

on

fire 2946038 640 640x426

Wasu mutane huɗu sun rasa rayukansu sakamakon wata mummunar gobara da ta tashi a gidan wani mutum mai suna Abubakar Idi, a Rugan Badali Fulani, Ƙaramar Hukumar Karasuwa ta Jihar Yobe.

Waɗanda suka mutu sun haɗa da matan Idi guda biyu da kuma ’ya’yansa mata guda biyu, waɗanda gobarar ta rutsa da su a cikin gidan.

An Kama Wani Matashi Da Ya Je Zana Wa Mahaifinshi Mai Shekaru 67 Jarrabawar Ƙarin Girma

Lamarin ya faru ne a ranar 21 ga Agusta, 2026, inda Rundunar ’Yan Sandan Jihar Yobe ta ce binciken farko ya gano cewa ɗan gidan mai shekara tara ne ake zargin ya kunna wutar.

Kakakin Rundunar, ASP Yusuf Ali, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.

A cewar sanarwar, hedikwatar ’yan sandan Karasuwa ta samu kiran gaggawa kan gobarar, lamarin da ya sa Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, CP Unman Jibrin, ya umarci sashen Violent Crime Response Unit (VCRU) da ya gudanar da cikakken bincike.

Advertisement

Rundunar ta ce a yayin binciken, yaron ya amsa cewa shi ne ya kunna wutar, yana mai cewa ya yi hakan ne domin ramuwar gayya bayan mahaifinsa ya yi masa duka kwana guda kafin faruwar lamarin.

An ce mahaifin ya yi wa yaron dukan ne bayan zargin cewa ya saci kaza.

Sanarwar ta ce gobarar ta kashe matan Abubakar Idi guda biyu da ’ya’yansa mata guda biyu, waɗanda suke cikin gidan a lokacin da gobarar ta tashi.

Rundunar ta bayyana cewa binciken na gab da kammalawa, inda daga bisani za a miƙa yaron ga hukumomin da suka dace domin ɗaukar matakin da doka ta tanada.

 

 

Advertisement

LEADERSHIP

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending