Connect with us

News

Ƙungiyar Academic Cycle Ta Jaddada Goyon Bayanta Ga Gwamnatin Kano Kan Bunƙasa Harkar Ilimi A Jihar 

Published

on

IMG 20261007 142101 263

Ƙungiyar malaman jami’o’i da masu koyarwa a manyan makarantu ta Academic Cycle ta bayyana cikakken goyon bayanta ga manufofin gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, musamman a fannin ilimi da binciken kimiyya.

Ɗaya daga cikin jiga-jigan ƙungiyar, Kabiru Dukawa, ya bayyana cewa an kafa Academic Cycle sama da shekaru 20 da suka gabata da nufin bayar da gudunmawa wajen inganta harkar ilimi da samar da ci gaba a Jihar Kano.

Kwamitin Kar-ta-kwana Na Yaki Da Ta’ammali Da Miyagun Kwayoyi Da Daba Ya Kama Mutum Da Kwalaben Kodin 151 A Kano

Dukawa ya ce ƙungiyar ta kasance tana fafutukar ganin an inganta tsarin ilimi tare da wayar da kan al’umma kan muhimmancin ilimi wajen samar da ci gaba mai ɗorewa.

Ya bayyana cewa ƙungiyar tana da kyakkyawar hulɗa da ɗalibai, tana kuma ƙoƙarin ganin an samar da ingantaccen yanayi da zai taimaka wajen samun nasarar karatun ɗalibai.

A cewarsa, Academic Cycle ta kuma nuna goyon bayanta ga tsare-tsaren gwamnatin Kano na bunƙasa ilimi da bincike, tana mai cewa irin waɗannan matakai za su taimaka wajen haɓaka ilimi a jihar.

Advertisement

Dukawa ya ce ƙungiyar za ta ci gaba da ba da gudunmawarta wajen tallafa wa duk wani shiri da zai inganta ilimi da samar da damar ci gaba ga matasa.

A nasa jawabin, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya ce masu ilimi suna da muhimmiyar gudunmawa wajen samar da ci gaba a jihar.

Waiya ya ce ya kamata malamai da sauran masu ilimi su ƙara shiga cikin harkokin ci gaban al’umma, musamman wajen tunkarar matsalolin da ke addabar matasa.

Ya bayyana cewa ya kamata masu ilimi su kasance cikin masu taka rawar gani wajen wakiltar muradun al’umma, maimakon barin wannan dama ga mutanen da ba su da isasshen ilimi ko ƙwarewa.

Kwamishinan ya kuma yi kira ga malamai da su ƙara mayar da hankali wajen wayar da kan matasa kan illolin fadan daba da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi, yana mai cewa ilimi na da muhimmiyar rawa wajen dakile waɗannan matsaloli.

Ya ce haɗin gwiwar malamai, gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki na da matuƙar muhimmanci wajen samar da ingantaccen tsarin ilimi da kuma ci gaban Jihar Kano.

Advertisement

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending