Connect with us

News

Ƴan Bindiga Sun Hallaka Mutane 17 A  Zamfara 

Published

on

IMG 20261007 183919 165

‎’Yan bindiga sun kashe akalla mutane 17 a wasu hare-hare da suka kai wani wurin haƙar zinare da kuma wani ƙauye a ƙaramar hukumar Maru ta Jihar Zamfara.

‎Rahotanni sun ce maharan ɗauke da makamai, waɗanda ke kan babura, sun kai harin ne a ranar Litinin a wani wurin haƙar ma’adinai da ke wajen ƙauyen Bindin.

‎Kwamishinan Ƴansandan Kano Ya Bukaci Sarki Aminu Ado Ya Janye Shirin Sa Na Hawan Fatahu Yakasai 

‎A cewar hukumomin yankin, maharan sun fara kai hari kan masu haƙar zinare, inda suka harbe mutane biyar har lahira.

‎Daga bisani, maharan sun shiga ƙauyen, inda suka yi arangama da jami’an tsaro. A yayin arangamar ne aka kashe wasu mutane 12, lamarin da ya ɗaga adadin waɗanda suka rasa rayukansu zuwa 17.

‎Mai ba da shawara kan harkokin ƙauyen, Abdullahi Musa Mutunji, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa harin na iya kasancewa ramuwar gayya ne.

Advertisement

‎Ya ce wasu masu haƙar ma’adinai sun kashe wani ɗan bindiga da ya yi musu barazana, wanda hakan ya jawo harin.

 

 

TRT AFRIKA 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending