Connect with us

News

Jami’an Ƴansanda Sun Kama Wani Mutum Kan Zargin Kona Gidan Yayansa A Jigawa 

Published

on

Rundunar ƴan sandan Jihar Jigawa ta kama wani mutum mai shekaru 27, Abbas Ibrahim, bisa zargin cinna wa gidan babban yayansa wuta a Ƙaramar Hukumar Gwaram ta jihar.

Kakakin rundunar, SP Lawan Shiisu Adam, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, 6 ga Oktoba, 2026.

Jami’an Yansandan  Sun Kama Mutum 13 Da Ake Zargin ‘Yan Kungiyar Asiri Ne A Anambra

A cewar sanarwar, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:30 na dare a ranar 29 ga Satumba, 2026, a ƙauyen Nassarawa da ke Ƙaramar Hukumar Gwaram.

Rundunar ta ce wanda ake zargin ya shiga gidan babban yayansa, Basiru Shuaibu, mai shekaru 25, inda ya zuba fetur a cikin ɗakinsa sannan ya cinna masa wuta.

An ce Basiru da matarsa sun samu munanan raunuka sakamakon gobarar, inda aka kai su wajen wani mai maganin gargajiya domin samun kulawa.

Advertisement

Sai dai Basiru ya rasu daga baya sakamakon raunukan da ya samu.

Rundunar ta ce an kama Abbas a garin Sara da ke Ƙaramar Hukumar Gwaram, inda ya yi ikirarin cewa ba ya cikin hayyacinsa a lokacin da lamarin ya faru.

A halin yanzu, ana gudanar da bincike kan lamarin a Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jiha (SCID) da ke Dutse.

Haka kuma, an gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu domin fuskantar shari’a.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending