News
Jami’an Yansandan Sun Kama Mutum 13 Da Ake Zargin ‘Yan Kungiyar Asiri Ne A Anambra
Rundunar ’yansandan Jihar Anambra ta ce ta kama mutane 13 da ake zargi da kasancewa mambobin ƙungiyoyin asiri, a wasu samame daban-daban, tare da ƙwato bindigogi, harsasai, tsafi, kayan da ke da alaƙa da ƙungiyoyin asiri, miyagun ƙwayoyi, makamai masu haɗari da kuma wata mota da aka sace.
A cikin wata sanarwa, Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, Tochukwu Ikenga ya ce jami’an sashen ’yansandan Okpoko sun kai samame a ranar 30 ga Satumba, bayan samun sahihan bayanan sirri, a wani wurin da ake zargin ɓoyayyen sansanin masu aikata laifuka ne kusa da Kasuwar Coca-Cola da ke Okpoko.
Wani Yaro Mai Shekara 9 Ya Ƙona Gidan Mahaifinsa Bayan An Zarge Shi Da Satar Kaza A Yobe
Sanarwar ta ce bayanan da wanda ake zargin ya bayar sun taimaka wa ’yan sanda wajen gano wasu mutane da ake zargin suna da alaƙa da ƙungiyar.
