News
Saƙon “Renewed Hope” Ya Isa Ga Jama’a — Waiya Ya Bukaci Mukarraban Shugaba Tinubu Daga Arewa Su Kai Saƙon Gwamnati Ga Jama’a
Wani jagoran ƙungiyar Nigeria Forward Project, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, ya yi kira ga mukarraban gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu daga Arewacin Najeriya da su ƙara ƙoƙari wajen bayyana manufofi da ayyukan gwamnatin tarayya ga jama’a.
Waiya ya ce ya kamata waɗanda aka naɗa a mukamai daga Arewa su kai saƙon gwamnatin zuwa matakin ƙasa, maimakon ya tsaya a Abuja kawai.
ASUU-KUST Ta Yabawa Gwamnatin Kano Kan Aiwatar Da Yarjejeniyar 2025
A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, ya ce ya kamata mukarraban gwamnatin su je wuraren da jama’a ke rayuwa, ciki har da kasuwanni, gonaki, jami’o’i da sauran al’ummomi, domin bayyana musu tasirin manufofin gwamnatin.
Kiran nasa na zuwa ne bayan Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ya buƙaci ministoci, masu ba da shawara da shugabannin hukumomin gwamnatin tarayya da su inganta yadda suke isar da bayanai kan ayyuka da manufofin gwamnati ga ’yan Najeriya.
Akume ya yi wannan kira ne a wani taron mukarraban gwamnatin tarayya da aka gudanar a Abuja.
A cewar Waiya, yayin da ake tunkarar zaɓen shugaban ƙasa na 2027, bai kamata yunƙurin wayar da kan jama’a ya kasance batun siyasa kawai ba.
Ya ce ya kamata a yi amfani da wannan dama wajen bayyana wa ’yan Najeriya abin da Renewed Hope Agenda ta ƙunsa da kuma yadda manufofin gwamnatin ke shafar rayuwarsu.
“Zaɓen 2027 zai kasance hannun ’yan Najeriya. Za su yanke hukunci ne bisa abin da suka gani, suka fuskanta kuma suka fahimta,” in ji shi.
Waiya ya kuma bukaci mukarraban gwamnatin da su bayyana abubuwan da gwamnati ta cimma tare da gabatar da bayanai kan manufofin da take aiwatarwa.
Ya ce saƙon Renewed Hope bai kamata ya kasance taken gwamnati kawai ba, sai dai ya zama wani abu da jama’a za su iya gani da kuma fahimta a rayuwarsu.
Waiya, wanda shi ne Co-Convener na Nigeria Forward Project, ya sanya hannu kan sanarwar ranar 8 ga Oktoba, 2026.
