Connect with us

News

ASUU-KUST Ta Yabawa Gwamnatin Kano Kan Aiwatar Da Yarjejeniyar 2025

Published

on

images (1)

Daga Muhammad Kabir, Kano

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), reshen Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Kano (KUST), Wudil, ta yaba wa Gwamnatin Jihar Kano bisa yadda ta mayar da yarjejeniyar da Gwamnatin Tarayya ta ƙulla da ƙungiyar a shekarar 2025 doka tare da aiwatar da ita.

Ƙungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar bayan taron majalisar ƙungiyar da aka gudanar ranar Litinin, 5 ga Oktoba, 2026.

Jirgin Dakarun Sojin Sama Ya Yi Saukar Gaggawa A Gonaki A Benue

A cewar ASUU-KUST, Kano na daga cikin jihohin farko a ƙasar nan da suka mayar da yarjejeniyar ta 2025 doka tare da aiwatar da ita gaba ɗaya.

Ƙungiyar ta kuma yaba wa gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf kan matakan da take ɗauka wajen inganta jin daɗin ma’aikatan jami’ar da kuma kyautata yanayin aikin malamai.

Advertisement

ASUU-KUST ta ce tana kuma amincewa da irin gudunmawar da gwamnatin jihar ke bayarwa wajen bunƙasa jami’ar da kuma inganta jin daɗin malaman jami’ar.

Shugaban ƙungiyar ASUU na KUST, Dakta Aliyu Yusuf Ahmad, da Sakataren ƙungiyar, Dakta Yusuf Shehu, ne suka sanya hannu kan sanarwar.

Ƙungiyar ta bayyana wannan matsayi ne a daidai lokacin da ake bikin Ranar Malamai ta Duniya, tare da cika shekaru 60 da amincewa da shawarwarin ILO/UNESCO kan haƙƙoƙin malamai, nauyin da ke kansu da kuma yanayin aikin koyarwa.

ASUU-KUST ta buƙaci ci gaba da jajircewa wajen aiwatar da manufofi da shirye-shiryen da za su ƙara inganta jin daɗin ma’aikatan jami’o’i tare da bunƙasa ingancin ilimi a Jihar Kano.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending