News
Kotu Ta Yi Watsi Da Karar El-Rufai Ta Neman Hana DSS, EFCC da ICPC Dakatar Da Asusunsa Da Kwace Kadarorinsa
Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shigar domin hana hukumomin tsaro da yaƙi da cin hanci daskarar da asusun bankinsa ko ƙwace kadarorinsa.
Jaridar Independent ta ruwaito cewa Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ce ta yanke hukuncin, inda ta bayyana ƙarar a matsayin wadda ba ta da tushe kuma aka shigar da ita ta hanyar da ta saɓa wa tsarin gudanar da shari’a.
Jami’an Ghana Da Na FBI Sun Kama Mutum 130 Kan Zargin Alaka Da Zambar Sama Da Naira Biliyan 13
Kotun ta ce El-Rufai ya riga ya shigar da makamanciyar ƙara a Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya (FCT), lamarin da ya sa sake shigar da wata ƙarar mai kama da ita ya zama amfani da kotu ta hanyar da ba ta dace ba.
Hukumomin da ƙarar ta shafa sun haɗa da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da sauran Laifukan da Suka Shafi Hakan (ICPC), Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC), Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) da kuma Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya.
Mai Shari’a Abdulmalik ta kuma bayyana cewa ba za a yi amfani da kotu wajen hana hukumomin da doka ta ba wa ikon gudanar da bincike sauke nauyin da ke kansu ba.
Haka kuma, kotun ta amince da hujjar cewa ƙarar ba ta nuna wata sahihiyar hujjar da za ta ba da damar ɗaukar matakin shari’a a kan EFCC, DSS da Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya ba, don haka ta cire sunayensu daga cikin waɗanda ake ƙara.
A cikin ƙarar, El-Rufai ya nemi kotun ta hana hukumomin daskarar da asusun bankinsa, ƙwace ko kwace kadarorinsa, ko neman umarnin ƙwace kadarorin har sai an kammala sauraron ƙarar.
Tsohon gwamnan ya kuma nemi kotun ta tabbatar da cewa kuɗin alawus ɗin sallamarsa da ya samu bayan kammala wa’adinsa na mulki daga shekarar 2015 zuwa 2023 kuɗi ne da ya samu bisa doka, kuma kadarorin da ya saya da su mallakarsa ne ta halal.
Bugu da ƙari, El-Rufai ya nemi a ba shi diyyar naira biliyan ɗaya bisa zargin barazanar take masa haƙƙoƙinsa, tare da naira miliyan 100 a matsayin kuɗin shari’a.
Sai dai kotun ta yi watsi da ƙarar, tana mai cewa ta samo asali ne daga zato kuma ba ta da isasshen tushe na shari’a.
