Connect with us

News

Ma’auratan Da Aka Yi Garkuwa Da Su Tare Da Jaririyarsu A Kaduna Sun Roƙi Gwamnati Ta Kuɓutar Da Su

Published

on

Ahmed Zakka his wife and child who were kidnapped from their house at Millennium City in Kaduna State last week 768x438

Wasu ma’aurata da aka yi garkuwa da su tare da jaririyarsu mai watanni shida a jihar Kaduna sun roƙi gwamnati da jami’an tsaro su taimaka wajen kuɓutar da su daga hannun masu garkuwa da mutanen.

Ma’auratan sun yi wannan roƙo ne a cikin wani bidiyo da ya yaɗu a kafafen sada zumunta, inda aka ga mijin mai suna Ahmed Abubakar Zakka, sanye da rigar matarsa, yana riƙe da jaririyar, yayin da matarsa ke zaune kusa da shi.

Allah Yayiwa Ismail Garba Gwammaja rasuwa, Tsohon Kakakin Ma’aikatar Lafıya Ta  Kano

An kuma ga ɗaya daga cikin masu garkuwa da mutanen ya nufi Zakka da bindiga.

An sace ma’auratan ne tare da jaririyarsu a ranar 6 ga Oktoba, 2026, lokacin da ’yan bindiga suka kai hari a Alrahus Estate da ke Millennium City, ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna inda suka kutsa cikin gidan Zakka tare da yin awon gaba da shi, matarsa da jaririyarsu.

 

Advertisement

 

DAILY TRUST 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending