Labarai
An Kama Ɗan Wasan Golf Ɗan Afirka Ta Kudu Da Mai Girki ’Yar Kenya Da Tabar Wiwi Kilo 50 A Legas

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta kama wani ɗan wasan golf ɗan Afirka ta Kudu, Grobler Henlo, mai shekaru 37, da wata mai girki ’yar Kenya, Abubakar Njambi, mai shekaru 25, bisa zargin safarar tabar wiwi mai nauyin kilo 50.40 zuwa Najeriya.
Kakakin hukumar, Femi Babafemi, ya bayyana cewa an kama mutanen ne a filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas a watan Oktoba, bayan an gano fakiti 46 na tabar wiwi mai ƙarfi da aka ɓoye a cikin akwatuna biyu.
Dakarun Soji Sun Kuɓutar Da Yara 18 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Kaduna
Hukumar ta ce bincike ya gano cewa mutanen sun sauya alamomin akwatunansu domin ɓoye ainihin masu kayan, inda Henlo ya riƙe akwatuna masu alamun Njambi, ita kuma ta karɓi akwatuna masu alamun Henlo.
NDLEA ta ce Henlo ya bayyana cewa wani mutum ne ya ɗauke shi aiki a Afirka ta Kudu, tare da yi masa alƙawarin rand 5,000 idan ya kai kayan Najeriya.
Njambi kuwa ta ce an ɗauke ta aiki ne da alƙawarin dala 8,000, bayan wata ƙawarta ta shawo kanta ta shiga aikin.
An kama Njambi a ranar 15 ga Oktoba a filin jirgin saman Legas, lokacin da take ƙoƙarin komawa Kenya.
A wasu samamen da hukumar ta gudanar a jihohi daban-daban, ta kuma kwato miyagun ƙwayoyi, ciki har da tramadol, diazepam, tabar wiwi da hodar iblis, tare da kama wasu mutane da ake zargi da safarar su.
A jihar Ondo, NDLEA ta tare tabar wiwi mai nauyin kilo 1,045 da ake zargin ana kaiwa Kano, inda ta kama mutum huɗu da ake zargi da hannu a safarar kayan.
Shugaban NDLEA, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya), ya ce kama ɗan wasan golf da mai girkin na nuna yadda ƙungiyoyin safarar miyagun ƙwayoyi ke amfani da ƙwararru wajen kai kayansu.
Ya gargaɗi masu safarar miyagun ƙwayoyi cewa babu sana’a ko matsayin mutum da zai hana jami’an tsaro bincikarsa a tashoshin shigowa Najeriya.
