Labarai
Dakarun Soji Sun Kuɓutar Da Yara 18 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Kaduna

Dakarun Sojojin Najeriya sun kuɓutar da yara 18 daga cikin 22 da wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Jihar Kaduna.
An yi garkuwa da yaran, waɗanda mambobi ne na ƙungiyar Boys’ and Girls’ Brigade, a safiyar Lahadi, 22 ga Nuwamba, 2026.
Ya Kamata A Tube Duk Wani Sarki Da Aka Samu Da Laifin Rashin Da’a —Sheikh Ahmad Gumi
Lamarin ya faru ne a yankin Mother-Cat, da ke tsakanin Kachia da Kajuru, lokacin da yaran ke gudanar da tafiyar motsa jiki da sanyin safiya.
Rahotanni sun ce wasu ’yan bindiga sun tare yaran tare da yin awon gaba da su zuwa wani wuri da ba a sani ba.
Sai dai dakarun Sojojin Najeriya na ƙarƙashin Sub-Sector 5, runduna ta 1, waɗanda ke aiki a ƙarƙashin Sector 1 na Operation FANSAN YAMMA, sun shiga aikin ceto yaran nan take bayan samun kiran neman agaji.
Sojojin sun bi sawun waɗanda suka yi garkuwa da yaran zuwa yankin bakin Kogin Rehina, inda suka gudanar da samame tare da kuɓutar da yara 18 bayan mahara sun yi watsi da su.
An ce nasarar kuɓutar da yaran ta biyo bayan gaggawar ɗaukar matakin sojoji da kuma matsin lambar da suka ƙara wa masu garkuwa da su yayin da suke tserewa.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a bayyana inda sauran yara huɗu suke ba, yayin da kuma ba a bayar da cikakken bayani kan ko an kama wasu daga cikin waɗanda ake zargi da aikata laifin ba.
