Connect with us

Labarai

Adadin Waɗanda Suka Mutu A Rikicin Kambari Da Fulani Ya Kai 74  —Gwamnan Neja

Published

on

Niger State governor Umar Bago 768x512
Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Adadin mutanen da suka mutu sakamakon rikicin da ya ɓarke tsakanin masu sintirin sa-kai na al’ummar Kambari da makiyayan Fulani a ƙaramar hukumar Borgu ta jihar Neja ya ƙaru zuwa 74.

Gwamnan jihar, Mohammed Umaru Bago, ne ya bayyana hakan yayin ziyarar jajantawa da ya kai wa Sarkin Borgu, Alhaji Halilu Sani Dantoro, a fadarsa da ke garin New Bussa.

BAYAN WATA SHIDA: Shugaba Tinubu Ya Yi Alƙawarin Kuɓutar da Ɗaliban Da Aka Yi Garkuwa Da Su A  Borno

Rikicin ya samo asali ne bayan wani hari da ƴan bindiga suka kai ƙauyen Lumman-Ba’are, inda suka kashe dagacin garin, Malam Bawa Muhammad, matarsa da ƴaƴansa uku, tare da ƙona fadarsa.

Bayan harin ne wasu masu sintirin sa-kai suka kai harin ramuwar gayya garin Gada Oli bisa zargin cewa maharan sun fito daga yankin, lamarin da ya haddasa arangama da asarar rayuka.

Gwamna Bago ya yi kira ga ɓangarorin da abin ya shafa da su ajiye makamansu tare da rungumar zaman lafiya, yana mai sanar da cewa gwamnati za ta biya diyyar naira miliyan biyu ga iyalan kowane mutum daga cikin iyalai 74 da suka rasa ƴan uwansu.

Advertisement

Ya kuma bayyana shirin sake gina wuraren da aka lalata tare da ƙaddamar da shirin afuwa ga masu riƙe da makamai ba bisa ƙa’ida ba, domin su miƙa su ga hukumomi.

A wani mataki na ƙarfafa tsaro, Sufeto-Janar na Ƴansandan Najeriya, Olatunji Rilwan-Disu, ya bayar da umarnin tura ƙarin jami’an rundunar yaƙi da ta’addanci (CTU) zuwa yankin.

Mataimakin Sufeto-Janar na Ƴansanda, Shehu Umar Nadada, wanda ya wakilci IGP, ya gargaɗi al’ummomin yankin da kada su bari hare-haren ƴan bindiga su rikide zuwa rikicin ƙabilanci.

Shi ma Kwamishinan Ƴansandan jihar, Salisu Bello-Fago, ya gargaɗi jami’an tsaro da kada su yi amfani da halin rashin tsaron wajen cin zarafi ko karɓar kuɗi daga mutanen da rikicin ya raba da muhallansu.

 

 

Advertisement

DAILY TRUST 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending