Labarai
Hare-Haren Siyasa 124 Sun Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 22 Cikin Watanni Huɗu — Rahoto

Ƙungiyar Kimpact Development Initiative (KDI), ta bayyana cewa hare-haren siyasa guda 124 da suka auku a Najeriya cikin watanni huɗu, sun yi sanadin mutuwar mutane 22.
Ta bayyana haka ne yayin da ake tunkarar babban zaɓen da aka shirya gudanarwa ranar 16 ga watan Janairun 2027.
Adadin Waɗanda Suka Mutu A Rikicin Kambari Da Fulani Ya Kai 74 —Gwamnan Neja
Rahoton ya nuna cewa hare-haren siyasa na ƙara ƙamari a ƙasar, inda aka samu ƙaruwar su a baya-bayan.
KDI ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar a Abuja, inda ta nuna damuwarta kan yadda tashin hankali a dalilin siyasa ke ƙaruwa gabanin zaɓen.
Ƙungiyar, wadda ke mayar da hankali kan matasa, dimokuraɗiyya da inganta shugabanci, ta ce ta tattara bayanan ne daga ranar 1 ga watan Yuli zuwa 23 ga watan Nuwamba, 2026, ta hanyar shirinta na Nigeria Election Violence Education and Reporting (NEVER Project).
Ta ce hare-haren sun haɗa da tsoratarwa, cin zarafi, garkuwa da mutane, harbe-harbe da lalata kayayyakin yaƙin neman zaɓe.
Dangane da jihohin da abin ya fi shafa, rahoton ya nuna cewa Delta ce kan gaba wajen yawan mutanen da aka kashe, inda mutum biyar suka rasu a sakamakon hare-hare 10 da suka auku a jihar.
A Kano kuma an samu hare-hare 11 wanda a dalilin hakan mutum uku suka rasu, yayin da Ribas ta samu hare-hare 10 tare da mutuwar mutum ɗaya.
Rahoton ya kuma bayyana Kano, Delta, Ribas, Edo, Ondo da Kebbi a matsayin jihohin da ke fuskantar rikicin siyasa.
KDI ta ce hare-hare da cin zarafi sun kai kashi 46.8 cikin 100, yayin da lalata kadarori ya kai kashi 28.8.
Harbe-harbe sun kai kashi 10.2, tsoratarwa kashi 9, sannan garkuwa da mutane ta kai kashi 4.
Ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar tashin hankalin ya ƙaru yayin da ranar zaɓe ke ƙaratowa, musamman idan ba a ɗauki matakan gaggawa ba.
Ta danganta matsalar da rashin haƙuri tsakanin ’yan siyasa da magoya bayansu, da kuma amfani da kalaman tunzura jama’a.
Sai dai ta jaddada cewa rikicin ya shafi jam’iyyu daban-daban, don haka bai kamata a ɗora laifin kan wata jam’iyya guda ɗaya ba.
KDI ta kuma yi gargaɗin cewa magoya bayan jam’iyyu, ma’aikatan gwamnati, ’yan jarida da sauran jama’a na fuskantar barazana da tsoratarwa sakamakon amfani da ’yancinsu na dimokuraɗiyya.
Ƙungiyar ta buƙaci jam’iyyu da ’yan takara su tabbatar da cewa magoya bayansu sun gudanar da kamfen cikin lumana, tare da hana duk wani nau’in tashin hankali.
Haka kuma, ta buƙaci jami’an tsaro su ƙarfafa matakan tsaro tare da hukunta masu aikata laifuka ba tare da nuna bambanci ba.
Ta kuma yi kira ga INEC, ƙungiyoyin fararen hula, shugabannin addinai, sarakunan gargajiya da kafafen yaɗa labarai da su ƙara wayar da kan jama’a kan muhimmancin zaman lafiya yayin zaɓe.
KDI ta buƙaci ’yan Najeriya da su guje wa tashin hankali tare da kai rahoton duk wata barazana ga hukumomin da suka dace don ɗaukar mataki.
