Connect with us

News

Kwastan sun kama kayan sama da naira miliyan 90 a Kebbi

Published

on

Hukumar kwastan ta kasa ta ce ta kama haramtattun kaya iri daban-daban da aka yi satar shiga da su ƙasar waɗanda kuɗinsu ya kai naira N91,518,928 a Jihar Kebbi, cikin mako uku.

Babban jami’in hukumar na yanki Kwanturola B Oramalugo, wanda ya sheda wa manema labarai haka kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, ya ce jami’ansu sun kama lita 8,975 ta man fetur da aka zuba a jarkoki masu cin lita 25 daga hannun masu fasa ƙwauri.

Advertisement

Buhari Ya Ce A Ci Gaba Da Amfani Da Tsoffin Takardun N200

Ya ce sauran kayan da suka kama sun haɗa da buhun shinkafa ‘yar waje 189 da buhun sukari na waje 71 da dilar tufafi gwanzo 42 da buhun takalma shi ma gwanjo 36.

Akwai kuma katan-katan na man shafawa mai sa fata haske guda 74 da batiran samar da lantarki daga hasken rana guda 110 da katan-katan na magani 105 da ƙananan motoci bakwai da kuma tirela da suma na waje ne.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending