News
2026: JAMB Ta Aiyana Maki 150 Mafi Karanci Maki Na Shiga Jami’a A Najeriya
Hukumar shirya jarabawar shiga manyan Makarantu a Najeriya JAMB ta ayyana maki 150 a matsayin mafi karancin makin da dalibai za su samu, masu neman gurbin shiga manyan makarantu a fadin Ƙasar a shekarar 2026.
An cimma matsaya ne a ranar Litinin a taron tsara manufofi kan shiga manyan makarantu na shekarar 2026 da aka gudanar a birnin tarayya Abuja inda ministan ilimi Tuniji Alausa, shugabannin jami’o’i Kwalejojin ilmi da masu ruwa da tsaki a bangaren ilmin manyan makarantu daban-daban ne su ka halarta.
ASUU Ta Yi Barazanar Tsunduma Yajin Aiki
JAMB ta ce maki 150 a matsayin mafi karancin makin shiga kwalejojin jinya, ya yin da kwalejojin kimiyya da fasaha ya kasance maki 100 cikin maki 400 na jarabawar UTME.
Hukumar ta bayyana ce sabo tsarin na nufin dukkan wani dalibi da ke neman gurbi a manyan makarantun Ƙasar nan a shekarar 2026, ya zama wajibi ya samu akalla maki 150 a jarabawar ta JAMB.
Ta kara da cewa makin da a ka kayyade, na da nufin cewa babu wata makarantar gaba da sakandare da za ta bai’wa dalibi gurbin karatu matukar makinsa bai kai yadda ake bukata ba.
Sai dai hukumar ta ce makarantu na da damar sanya maki fiye da wanda a ka kayyade ga masu son shiga manyan makarantun.
