News
ASUU Ta Yi Barazanar Tsunduma Yajin Aiki
Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), ta yi barazanar tafiya yajin aiki na sai-baba-ta-gani kan shirin gwamnatin tarayya na soke wasu kwasa-kwasan ilimi da aka kira ‘ba su da muhimmanci’ a jami’o’in Nijeriya.
Comrade Christopher Piwuna, Shugaban ASUU, ne ya sanar da shirin yajin aikin a taron Majalisar Zartarwa ta Kasa (NEC), wanda aka gudanar a Jami’ar Modibbo Adama Yola, ranar Litinin 11 ga watan Mayu, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Tsunduma Yajin Aiki
A cikin sanarwar da ya fitar, Piwuna ya nuna damuwa kan yadda gwamnati ke jan kafa wajen warware matsalolin da suka shafi malaman jami’o’i, ciki har da rike albashin watanni uku da rabi, rashin biyan kudaden karin girma, da kuma bashin karin albashi na kaso 25 zuwa 35 cikin dari.
Ya ce rashin daukar mataki daga bangaren gwamnati na kara haddasa takaici da bacin rai a tsakanin malaman jami’o’i, lamarin da ka iya haifar da sabon yajin aiki idan ba a magance matsalolin cikin gaggawa ba.
“ASUU na kira ga duk masu kishin kasa da su matsa wa gwamnatocin tarayya da jihohi lamba domin su cika alkawuran da suka dauka tare da warware sauran matsalolin da suka rage domin kare makomar dalibai da tsarin ilimi,” in ji shi.
Rahotanni sun nuna cewa yarjejeniyar da aka cimma tsakanin ASUU da gwamnati a shekarar 2025 an yi fatan za ta kawo karshen rikicin da ya dauki sama da shekaru 16 ana yi kan yarjejeniyar shekarar 2009.
Sabuwar yarjejeniyar ta kunshi karin albashi da kaso 40 cikin dari ga malaman jami’o’i, inganta tsarin fansho da kuma sake fasalin alawus-alawus na aikin koyarwa domin rage yawan yajin aiki a jami’o’in gwamnati.
Sai dai bayan shafe watanni biyar da fara aiwatar da yarjejeniyar, gwamnatin tarayya ba ta cika nata bangaren ba, lamarin da ke kara jefa makomar jami’o’in gwamnati cikin rashin tabbas.
