Connect with us

News

Harin Dakarun Sojin Chadi Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Ɗimbin Masunta ’Yan Najeriya

Published

on

Wani Jirgin Rundunar Sojin Saman Najeriya Ya Hallaka Mutane Da Dama A Sokoto 

Rahotanni daga gaɓar Tafkin Chadi sun bayyana cewa wani farmaki da sojin saman ƙasar Chadi suka kai ya yi sanadiyyar mutuwar ɗimbin masunta, mafi yawansu ’yan Najeriya masu sana’ar kamun kifi a yankin.

Lamarin ya faru ne kwanaki uku bayan da mayaƙan Boko Haram suka kai hari kan sansanin sojin Chadi tare da kashe aƙalla dakaru 24, abin da ya sa mahukuntan birnin Ndjamena suka umarci rundunar sojin saman ƙasar da ta ƙaddamar da hare-hare kan waɗanda ake zargin mayaƙa ne da ke fakewa a yankunan tafkin suna gudanar da harkokin kamun kifi.

Advertisement

Iran Ta Rataye Mutumin Da Ya Yi Wa Amurka Da Isra’ila  Leƙen Asiri

Shaidu da dama, ciki har da ’yan sa-kai masu taimakawa wajen kare fararen hula daga hare-haren Boko Haram, sun bayyana cewa farmakin ya hallaka gomman mutane, duk da cewa har yanzu ba a tantance adadin waɗanda suka mutu ba.

Advertisement

Wani ganau ya ce tun daga ranar Juma’ar da ta gabata ne sojojin saman Chadi suka fara kai hare-haren kan wasu tsibirai da ke ƙarƙashin yankunan Najeriya da kuma Jamhuriyar Nijar.

A cewarsa, daga cikin waɗanda suka mutu akwai masunta da ke gudanar da sana’arsu da izinin mayaƙan Boko Haram bayan biyan harajin da ƙungiyar ke karɓa daga gare su.

Advertisement

Wani jagoran al’umma daga Tsibirin Shuwa, ɗaya daga cikin wuraren da aka kai wa harin, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa baya ga waɗanda aka tabbatar da mutuwarsu, akwai wasu mutane kusan 40 da suka ɓace.

 

Advertisement

 

AMINIYA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending