News
Ragunan Layya Sun Yi Tashin Gwauron Zabo
Yayin da ya rage mako guda a yi Babbar Sallah, farashin raguna ya yi tashin gwauron zabo a sassa daban-daban na Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Dillalan dabbobin layya sun bayyana suna cewa mutane da yawa na zuwa su tambayi farashi, amma su tafi ba tare da sun saya ba.
Kanawa Sun Yarda Da Tsarin NDC Kwankwasiyya’ — Hon. Sagir Wada Sinkin
Bincike ya nuna cewa farashin raguna a bana ya haura na bara sosai, lamarin da ya sa mutane da dama ke kokawa kan rashin ƙarfin sayen abin yin layya.
A kasuwar dabbobi da ke kan hanyar Abaji zuwa Lakwaja, ƙaramin rago da aka sayar tsakanin Naira 130,000 zuwa N150,000 a bara yanzu ya kai tsakanin N185,000 zuwa N200,000.
Matsakaicin rago kuma da aka sayar tsakanin N220,000 zuwa N250,000 a bara yanzu ya kai tsakanin N280,000 zuwa N320,000, yayin da manyan raguna suka kai har Naira 600,000 zuwa sama da miliyan ɗaya.
A wasu kasuwanni da ke ƙauyukan Abuja, masu saye sun fi karkata wajen sayen raguna kai tsaye daga makiyaya saboda sauƙin farashi idan aka kwatanta da sayen raguna a hannun dillalan da ke kawo dabbobin daga Arewa.
Masu sayar da ragunan sun danganta tashin farashin da rashin tsaro da kuma tsadar sufuri daga jihohin Arewa zuwa Abuja.
Wasu daga cikinsu sun kuma koka kan rashin ciniki duk da tashin farashin, suna cewa mutane da yawa na zuwa su tambayi farashi, amma su tafi ba tare da sun saya ba.
A gefe guda, wasu ma’aikata da mazauna Abuja sun ce tsadar rayuwa da bashin banki sun hana su samun damar sayen ragunan layya bana.
