Connect with us

News

Faɗan Daba Ya Yi Ajalin Jami’in Ɗan Sanda Mako Biyu Kafin Ritaya A Kano

Published

on

Wani jami’in ɗan sanda mai suna Sani S.O. da ke aiki a Ofishin ‘yan sanda na Hotoro a Jihar Kano, ya rasa ransa bayan wani rikicin daba da ya ɓarke a cikin birnin Kano.

Rahotanni sun nuna cewa marigayin ya mutu ne yayin da yake bakin ƙoƙarinsa na dakile rikicin da kuma kwantar da tarzomar da wasu da ake zargin ‘yan daba ne suka haddasa a wasu unguwannin birnin.

Advertisement

Shugaban Karamar Hukuma Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Jigawa 

Jaridar Wikki Times ta ruwaito cewa jami’in ya shiga tsakani domin hana rikicin ƙara faɗaɗa ne kafin ya samu munanan raunuka da suka yi sanadin mutuwarsa.

Advertisement

Lamarin ya jefa mazauna yankin da abokan aikinsa cikin alhini, musamman kasancewar saura makonni biyu kacal marigayin ya yi ritaya daga aikin ‘yan sanda bayan shafe shekaru yana hidimtawa ƙasa.

Wasu daga cikin abokan aikinsa sun bayyana shi a matsayin jami’i mai mutunci, ƙwazo da jajircewa wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a tsakanin al’umma.

Advertisement

Mutuwar jami’in ta sake tayar da hankali kan yadda ayyukan ‘yan daba ke ƙara yawaita a wasu sassan Kano, lamarin da jama’a ke ganin yana buƙatar ƙarin matakan tsaro daga hukumomi.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, hukumomin tsaro ba su fitar da cikakken bayani kan musabbabin rikicin ba, sai dai ana sa ran za a gudanar da bincike domin gano waɗanda ke da hannu a tayar da tarzomar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending