Connect with us

News

Kamfanin Maltina Ya  Ƙaddamar Da Shirin Wayar Da Kan Ɗalibai Kan Muhimmancin Karatun Kimiyya Da fasaha A Kano 

Published

on

IMG 20260520 112749 235

Kamfanin Maltina ya sake nuna jajircewarsa wajen tallafa wa harkar ilimi da cigaban matasa bayan ƙaddamar da wani gagarumin shiri na wayar da kan ɗalibai kan muhimmancin kimiyya da fasaha a makarantu 30 da ke faɗin Jihar Kano.

Shirin, wanda ya samu karɓuwa daga malamai da masu ruwa da tsaki a fannin ilimi, na da manufar ƙarfafa ɗalibai su mayar da hankali kan ilimin zamani domin gina kyakkyawar makoma tare da taimakawa cigaban tattalin arziki da al’umma baki ɗaya.

Advertisement

Manufar shirin ita ce gina matasa masu hangen nesa tare da samar da ƙwararrun ɗalibai da za su taimaka wajen cigaban ƙasa a nan gaba.

Faɗan Daba Ya Yi Ajalin Jami’in Ɗan Sanda Mako Biyu Kafin Ritaya A Kano

Advertisement

IMG 20260520 103340 744

Da yake jawabi yayin ƙaddamar da shirin, wakilin Kamfanin Maltina na Arewacin Najeriya, Kabiru Al-Kasim, ya bayyana cewa kamfanin ya ɗauki tallafa wa ilimi a matsayin wani muhimmin ɓangare na gudunmawar da yake bayarwa ga cigaban al’umma.

Ya ce wannan ba shi ne karo na farko da Maltina ke gudanar da irin wannan shiri a Kano ba, yana mai tabbatar da cewa kamfanin zai ci gaba da kawo shirye-shiryen da za su amfani matasa da ɗalibai.

Advertisement

“Maltina ta yi imanin cewa ilimi shi ne ginshiƙin cigaba, musamman a wannan zamani da duniya ta karkata zuwa kimiyya da fasaha,” in ji shi.

IMG 20260520 144547 067

Shi ma da yake nasa jawabin, Malam Sagiru Umar Dan Bare daga Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano, ya yaba wa Kamfanin Maltina bisa wannan gagarumar gudunmawa da yake bayarwa wajen ƙarfafa ilimi a jihar.

Advertisement

Ya ce Kano jiha ce mai tarihi wajen neman ilimi, don haka irin wannan shiri zai taimaka wajen ƙara wa ɗalibai ƙwarin guiwa da fahimtar muhimmancin karatun kimiyya da fasaha.

“A yau duniya gaba ɗaya ta dogara ne da ilimin kimiyya da fasaha, saboda haka wannan shiri na Maltina zai taimaka wajen shirya ɗalibanmu domin fuskantar ƙalubalen zamani,” in ji shi.

Advertisement

IMG 20260520 144522 702

Hakimin Rimin Gado kuma wakilin Sarkin Kano, Alhaji Auwal Mudi Yakasai, ya kuma yaba wa Kamfanin Maltina bisa rawar da yake takawa wajen cigaban ilimi da tallafa wa matasa a jihar.

Ya ce haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu irin Maltina na da matuƙar muhimmanci wajen samar da cigaba mai ɗorewa a harkar ilimi da tattalin arziki.

Advertisement

IMG 20260520 120436 616

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending