Connect with us

News

Wani Sashe Na Ginin Babban Masallacin Zariya Ya Rufta  ‎

Published

on

1779303141432

Mutane uku sun samu raunuka bayan wani sashe na Babban Masallacin Zariya da ake ci gaba da sake gininsa ya rufta a ranar Laraba yayin gudanar da aikin zuba siminti.

‎Lamarin ya faru ne a lokacin da ma’aikata ke aikin shimfiɗa decking a bene na biyu kusa da hasumiyar kudu ta masallacin, inda wani ɓangare na ginin ya kife ba zato ba tsammani.

‎Kamfanin Maltina Ya  Ƙaddamar Da Shirin Wayar Da Kan Ɗalibai Kan Muhimmancin Karatun Kimiyya Da fasaha A Kano 

‎Shaidun gani da ido sun shaida cewa nan take aka ceto waɗanda suka jikkata tare da garzaya da su zuwa wani asibiti da ke Zariya domin samun kulawar likitoci.

‎Rahotanni sun tabbatar da cewa babu asarar rai sakamakon hatsarin.

‎Bayan aukuwar lamarin, an killace wurin aikin domin kauce wa wata barazana, yayin da aka ga ma’aikata suna kwashe ɓaraguzan ginin da ya rufta.

Advertisement

‎Ƙoƙarin jin ta bakin injiniyan da ke kula da aikin bai yi nasara ba, domin wasu majiyoyi sun bayyana cewa ya raka waɗanda suka jikkata zuwa asibiti.

‎Sai dai mai magana da yawun Masarautar Zazzau, Malam Abdullahi Kwarbai, ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ce masarautar ba za ta yi tsokaci a kai ba a halin yanzu.

‎A cewarsa, tun da farko an miƙa aikin sake gina masallacin ga wata kwamitin fasaha, wadda daga bisani ta bai wa kamfanin ginin da ke gudanar da aikin ikon kula da wurin.

‎Ya ƙara da cewa an gudanar da bikin ƙaddamar da aikin kafin fara aikin sake gina masallacin.

‎“Saboda haka, a yanzu masarautar ba za ta yi ƙarin bayani kan batun ba,” in ji Kwarbai.

 

Advertisement

 

DAILY TRUST 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending