Connect with us

News

Ana Zargin Wani Da Kirkirar Hukumar Bogi, Da Nada Kansa Shugaba, Da Karbar Sama Da Naira Biliyan 1 Daga CBN

Published

on

FB IMG 1782977515241

Ana zargin Prince Adeniyi Adeyemi Matthew da ƙirƙirar wata hukuma mai suna Presidential Foreign Intervention Promotion Council (PFIPC) tare da naɗa kansa a matsayin Darakta Janara (DG).

Rahotanni sun ce hukumar ta samu ofis a sakatariyar tarayya, ta kuma buɗe asusu a babban bankin kasa (CBN), kuma aka ware mata Naira biliyan 1.303 a kasafin kuɗin shekarar 2026.

Ajiye Waya A Kan Gado A Lokacin Da Ake Caji Na Da Illa Ga Lafiya —Masani

Sai dai tun da fari, fadar shugaban kasa ta musanta lamarun , tana mai cewa ba ta taɓa amincewa da kafa irin wannan hukuma ba, kuma ba ta naɗa kowa a matsayin shugabanta ba.

To sai dai Prince Adeniyi ya musanta zargin, yana mai cewa kasancewar sunan hukumar a cikin kasafin kuɗin 2026 na nuna akwai buƙatar cikakken bincike domin gano gaskiyar lamarin.

Hukumomin gwamnati na fuskantar tuhuma don gudanar da cikakken bayani kan yadda aka ce hukumar ta samu shiga cikin kasafin kuɗin tarayya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending