Connect with us

News

Wata Mota Ta Faɗa Cikin Kogin Mayo-Ine A Ngurore

Published

on

IMG 20260702 094406 814

Wata mota ƙirar Sharon ta faɗa cikin kogin da ke ƙarƙashin gadar Mayo-Ine a garin Ngurore, Jihar Adamawa, a wani hatsari da ya faru da tsakar ranar Alhamis.

Wani mazaunin yankin kuma shaidan gani da ido, Ibrahim Ibi, wanda ke aikin loda yashi a kusa da gadar, ya shaida cewa motar ta kauce daga kan hanya, inda direban ya yi ƙoƙarin dawo da ita kan titin, amma hakan bai yi nasara ba kafin motar ta kutsa cikin kogin.

Ana Zargin Wani Da Kirkirar Hukumar Bogi, Da Nada Kansa Shugaba, Da Karbar Sama Da Naira Biliyan 1 Daga CBN

A cewarsa, abin da ya gani ya nuna cewa da alama direban ne kaɗai ke cikin motar a lokacin da hatsarin ya faru. Sai dai ya ce ba zai iya tabbatar da hakan a hukumance ba.

Ya ce mutanen da suka yi gaggawar isa wurin sun shiga cikin ruwan domin gudanar da aikin ceto tare da binciken motar, amma har zuwa lokacin da yake magana ba su gano wani mutum a cikinta ba.

Rahotannin farko sun nuna cewa motar na ɗauke da tayoyin gini da wasu kayan aiki. Haka kuma, an gano wasu takalma a cikin motar, lamarin da ya haifar da hasashen cewa watakila akwai wasu fasinjoji. Sai dai babu wata hukuma da ta tabbatar da wannan zargi.

Advertisement

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, hukumomin da abin ya shafa ba su fitar da wata sanarwa kan musabbabin hatsarin ko adadin mutanen da ke cikin motar ba.

 

 

Albarka Radio 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending