News
An Tsinci Gawar Wani Matashi Da Aka Yi Wa Yankan Rago A Kano
Al’ummar unguwar Badawa, da ke yankin Unguwar Gaya a Jihar Kano, sun shiga cikin firgici da alhini bayan da aka tsinci gawar wani matashi da ba a tantance ko wanene ba a cikin wani gida da babu kowa a cikinsa.
Wani mazaunin yankin, Yusuf Da’u Ibrahim, ya shaida cewa lamarin ya faru ne bayan wani maƙwabci ya garzaya wajen shugaban unguwa domin sanar da shi cewa wani mutum ya samu munanan raunuka kuma yana neman agaji.
A cewarsa, kafin jami’an ceto su isa wurin, an riga an sanar da Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano, inda jami’an suka isa wajen cikin gaggawa, suka kama wani da ake zargi da hannu a lamarin, sannan suka kwashe gawar mamacin zuwa asibiti.
Aminiya ta ruwaito cewa mamacin, wanda aka kiyasta yana da kimanin shekaru 28, ya samu mummunan rauni a wuya, lamarin da ake zargin ya yi sanadin rasuwarsa kafin a samu damar kai masa agajin gaggawa.
Yusuf ya ce mazauna yankin ba su san ko wanene mamacin ba, yana mai ƙara da cewa wannan shi ne karon farko da aka samu irin wannan mummunan lamari a unguwar.
Da aka tuntuɓi jami’in hulɗa da jama’a na Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce har zuwa lokacin tattaunawar bai samu cikakken rahoto kan lamarin ba, amma ya tabbatar da cewa rundunar za ta gudanar da bincike domin gano haƙiƙanin abin da ya faru.
Rundunar ‘yan sanda ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan musabbabin mutuwar matashin ko cikakken bayani game da wanda ake zargi ba zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.
-
News7 days ago
HAWAN DABA DA KILISA :Gwamnatin Kano Ta Ce Ba Za Ta Lamunci Kalaman Tada Zaune Tsaye Ba
-
News7 days ago
An Yi Garkuwa Da Fiye Da Mutum 80 A Cikin Mako Biyu A Arewacin Nijeriya — Rahoto
-
News5 days ago
Kwankwaso Ya Bukaci ’Yan Najeriya Su Ci Gaba Da Marawa Sauye-Sauyen Shugaba Tinubu Baya
