News
Kawu Sumaila Ya Ce Ya Aiwatar Da Ayyuka 102 A Kano Ta Kudu Cikin Shekara Uku
Sanata Sulaiman Abdurrahman Kawu Sumaila ya ce ya aiwatar da ayyuka da shirye-shiryen tallafa wa jama’a guda 102 a ƙananan hukumomi 16 na Mazabar Kano ta Kudu tsakanin shekarun 2023 zuwa 2026.
Sanatan ya bayyana hakan ne a wani taron tattaunawa da jama’a da aka gudanar a Kano, inda ya yi bayani kan yadda ya ce ya cika alkawuran da ya ɗauka a lokacin yakin neman zaɓen shekarar 2023.
Maulidi Na Taimakawa Wajen Tunar Da Al’umma Halayen Annabi —Malam Ibrahim Khaleel
A cewarsa, ayyukan sun shafi noma, ilimi, kiwon lafiya, ababen more rayuwa da kuma tallafa wa matasa da mata.
Sanata Kawu Sumaila ya ce an samar da rijiyoyin ban-ruwa sama da 6,000 da rijiyoyin burtsatse 300, yayin da aka mayar da hekta 1,297 zuwa filayen noma masu amfani da ban-ruwa.
Ya kuma ce an girka fitilun hasken rana guda 3,745 a sassa daban-daban na mazabar.
A fannin ilimi, sanatan ya ce ɗalibai 1,082 sun samu tallafin karatu da alawus na wata-wata.
Ya ƙara da cewa ɗaliban da ke karatun fannonin kiwon lafiya guda 437 su ma sun samu tallafi.
A fannin kiwon lafiya kuma, Kawu Sumaila ya ce an samar da gadaje, katifu da kabad guda 1,200 ga cibiyoyin lafiya.
Ya ce an kuma ɗauki nauyin gudanar da tiyata sama da 400 a Asibitin Zarewa Standard.
Game da ababen more rayuwa, sanatan ya ce an farfaɗo da aikin wata hanyar mota mai tsawon kilomita 19 mai rabe-raben hanya.
Ya ce an kuma aiwatar da ayyukan dakile zaizayar ƙasa da ambaliya guda 16, tare da samar da gadoji da magudanan ruwa 11.
A wani ɓangare na shirye-shiryen tallafa wa jama’a kuwa, Kawu Sumaila ya ce an raba motoci guda 916 ta wasu shirye-shiryen tallafi guda 10.
Sanatan ya ce har yanzu akwai wasu ayyuka da shirye-shirye da ake shirin aiwatarwa a Mazabar Kano ta Kudu.
Ya kuma yi kira ga al’ummar yankin da su ci gaba da goyon bayan jam’iyyar APC a zaɓen 2027.
