News
FMC Nguru: Likitoci Sun Shiga Jimami Bayan Rasuwar ’Ya’yan CMD
Babbar Daraktar Likitanci (CMD) ta Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya (FMC), Nguru, Jihar Yobe, Dakta Hadiza Usman Abdullahi, ta rasa ’ya’yanta tagwaye, Dakta Hadiya Usman da Dakta Aisha Usman, cikin tazarar kwanaki biyu.
Dakta Hadiya, wadda likita ce, ta rasu ranar Juma’a, yayin da tagwayarta, Dakta Aisha, wadda ke da digirin Doctor of Pharmacy (PharmD), ta rasu ranar Lahadi.
Akwai Malamai 300,000 Ba Su Da Ƙwarewar Koyarwa A Nijeriya —TRCN
Mahaifiyar ’yan matan ta tabbatar da rasuwarsu ne ta wasu saƙonni da ta wallafa a shafinta na WhatsApp, inda ta sanar da rasuwar ’ya’yanta.
Rasuwar ’yan matan ta jefa iyalansu, abokan aikinsu da sauran ’yan ƙungiyar likitoci cikin babban alhini.
Hadiya da Aisha sun kasance ƙwararrun ma’aikatan lafiya, inda ɗaya ke aiki a matsayin likita, yayin da ɗayar ke aikin fannin hada magunguna.
Rasuwar ’yan matan biyu cikin kwanaki biyu ta jawo jimami a tsakanin ’yan uwa, abokan aiki da sauran al’ummar fannin lafiya.
Tun bayan samun labarin rasuwar, sakonnin ta’aziyya da addu’o’i na ci gaba da isa ga iyalan marigayin.
Ana roƙon Allah Ya gafarta musu, Ya jikansu da rahama, Ya kuma bai wa iyalansu da ’yan uwansu haƙurin jure wannan babban rashi.
