Connect with us

News

Shugaba Tinubu Ya Ayyana Makokin Kwana Uku Kan Hatsarin Jirgin Sojoji A Ondo

Published

on

Screenshot 20261005 150158

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana makokin kwana uku ga jami’an Rundunar Sojin Saman Nijeriya da suka rasu a hatsarin jirgin sojoji na ranar Litinin..

Haka kuma, Shugaban ya umarci a sauke tutoci zuwa tsakiyar sanduna domin karrama jami’an da suka rasa rayukansu a sanadiyyar aukuwar lamarin.

Kano First Forum Ta Kai Ƙorafi Ga Ƴansanda Kan Kalaman Aminu Babba Dan Agundi

Kakakin Shugaban ƙasa Bayo Onanuga ne ya sanar da wannan umarni a wata sanarwa da ya fitar a ranar 5 ga Oktoba, 2026. Da fari Shugaban ya bayyana kaɗuwarsa kan hatsarin jirgin mai tashin angulu na Nigeria Air Force ATR-42 jet, wanda ya yi ajalin mutane da dama.

 

Manhaja ta ruwaito cewa, al’amarin ya auku ne a kusa da sansanin sojin sama da ke yankin Igbokoda na Jihar Ondo da lokacin da jirgin yake ɗauke da fasinjoji guda 25 da jami’an jirgi su bakwai, wanda ya ɗauko hanya daga Benin zuwa Legas.

Advertisement

Shugaba Tinubu ya aike da saƙon ta’aziyyarsa ga Shugaban Rundunar Sojin Sama Air Marshal Sunday Kelvin Aneke da dukkan jami’an rundunar.

Ya kuma bayar da umarnin a gaggauta fara gudanar da bincike kan abin sa ya sabbaba aukuwar lamarin da kuma ƙoƙarin kare sake faruwar irin haka a nan gaba. Rundunar Sojin za ta fitar da sunayen jami’an da iftila’in ya shafa bayan tattaunawa da iyalansu.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending