Connect with us

News

Akwai Malamai 300,000 Ba Su Da Ƙwarewar Koyarwa A Nijeriya  —TRCN

Published

on

2b874d0e 83ce 45f7 a689 576d53c0b6f7 1791207263039

Kusan malamai 300,000 daga cikin malamai 700,000 da ke aiki a Nijeriya ba su da cikakkiyar ƙwarewar koyarwa, in ji Majalisar Rajistar Malamai ta Nijeriya (TRCN).

Shugaban TRCN, Josiah Ajiboye, ne ya bayyana hakan, inda ya ce Jihar Kano kaɗai na da kusan malamai 25,000 da ba su da cikakkiyar cancantar koyarwa.

Kano First Forum Ta Kai Ƙorafi Ga Ƴansanda Kan Kalaman Aminu Babba Dan Agundi

Sai dai ya ce zuwa yanzu, kusan 8,000 daga cikin malaman da ba su da ƙwarewar sun samu horo tare da zama ƙwararrun malamai, sakamakon haɗin gwiwar gwamnatin jihar da TRCN.

Ya ce an tura malaman zuwa Cibiyar Horar da Malamai ta Nijeriya (NTI), kwalejojin ilimi da kuma shirye-shiryen Difloma a Ilimi ga waɗanda suka kammala karatun jami’a.

Ajiboye ya bayyana hakan ne a wani taron tattaunawa mai taken, “Koyarwa cikin ’yanci: Ƙarfafa Malaman Nijeriya domin Tunkarar Ƙalubalen Ƙarni na 21”, wanda aka shirya domin bikin Ranar Malamai ta Duniya.

Advertisement

Ya ce siyasantar da harkar ilimi na daga cikin manyan dalilan da ke haifar da shigar mutanen da ba su da cancantar koyarwa cikin aikin malanta.

A cewarsa, wasu gwamnonin jihohi da ’yan siyasa kan bai wa mutanen da ba su samu aikin yi ba aikin koyarwa domin faranta musu rai.

“Koyarwa sana’a ce da ke buƙatar shiri da ƙwarewa, don haka bai kamata a mayar da ita sana’ar da kowa zai iya shiga ba,” in ji shi.

Shugaban TRCN ya kuma nuna damuwa kan yanayin aikin da malamai ke fuskanta a ƙasar, musamman matsalar jinkirta karin girma da kuma rashin tanadin kuɗaɗen aiwatar da karin girman idan an amince da shi.

Ya kawo misalin Jihohin Oyo da Osun, waɗanda a baya suka yi fice wajen samun kyakkyawan sakamako a jarabawar ƙasa, amma a yanzu sakamakonsu ya ragu saboda rashin isasshen ƙarfafa wa malamai gwiwa.

Ya ce wasu jihohi ma sun taɓa bin malamai bashin albashi na tsawon watanni takwas.

Advertisement

Malamai sama da 611 aka kashe a Arewa maso Gabas

Da yake magana kan matsalar tsaro, Ajiboye ya ce malamai sama da 611 ne aka kashe a yankin Arewa maso Gabas tun bayan fara hare-haren Boko Haram a shekarar 2009.

Ya ce wasu malamai kusan 19,000 kuma sun rasa matsugunansu sakamakon hare-haren ƙungiyar ’yan ta’addan.

A cewarsa, hare-haren sun yi matuƙar kawo cikas ga harkar ilimi a yankin, lamarin da ya tilasta wa malamai da dama barin garuruwansu domin tsira da rayukansu.

Ya ƙara da cewa wasu daga cikin malaman sun koma wasu jihohin ƙasar, yayin da wasu kuma suka tsallaka zuwa ƙasashen da ke makwabtaka da Nijeriya.

 

Advertisement

 

TRT AFRIKA 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending