Connect with us

News

NLC ta caccaki Malami, ta ce Gwamna Idris ya kyautata wa ma’aikatan Kebbi

Published

on

IMG 20261005 WA0022

Daga Khadijat Saidu, Birnin Kebbi

 

Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC), reshen Jihar Kebbi, ta yi watsi da ikirarin ɗan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar ADC, Abubakar Malami, SAN, kan halin da ma’aikatan jihar ke ciki, tana mai cewa gwamnatin Gwamna Nasir Idris ta yi abubuwa da dama wajen inganta walwalar ma’aikata.

Shugaban NLC na Jihar Kebbi, Alhaji Murtala Usman, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a Birnin Kebbi, yayin da yake mayar da martani kan jawabin ranar ’yancin kai da Malami ya gabatar.

Kano First Forum Ta Kai Ƙorafi Ga Ƴansanda Kan Kalaman Aminu Babba Dan Agundi

Usman ya ce NLC ta yaba da wasu shawarwarin Malami da suka shafi mafi ƙarancin albashi, ƙarin girma, fansho, kiwon lafiya da shigar ma’aikata cikin harkokin mulki.

Advertisement

Sai dai ya ce ƙungiyar ba za ta amince da zargin cewa ma’aikatan jihar na cikin mawuyacin hali saboda rashin biyan fansho, rashin aiwatar da ƙarin girma da kuma yanke albashi ba bisa ƙa’ida ba.

Ya ce: “Aikin ƙwadago ya ginu ne kan gaskiya, hujjoji da tattaunawa da hukumomin da abin ya shafa, ba kan jita-jita ko maganganun siyasa marasa tushe ba.”

Shugaban NLC ya ce tun daga shekarar 2023 ƙungiyar ke tattaunawa da gwamnatin jihar ta hanyar sulhu da shawarwari domin magance matsalolin ma’aikata.

A cewarsa, tattaunawar ta haifar da wasu nasarori, ciki har da aiwatar da mafi ƙarancin albashi na N75,000, wanda ya fi N70,000 da aka amince da shi a matakin ƙasa.

Ya ƙara da cewa gwamnatin ta ci gaba da biyan albashi da fansho, tare da gyara wasu alawus-alawus na ma’aikata lokaci zuwa lokaci.

Usman ya kuma bayyana cewa gwamnatin ta ɗauki ma’aikatan lafiya 2,568 da malamai 2,000, tare da ƙara shekarun ritayar malamai, likitoci da likitocin dabbobi daga 60 zuwa 65, yayin da shekarun hidima suka tashi daga 35 zuwa 40.

Advertisement

Ya ce a fannin lafiya, an gyara manyan asibitoci da cibiyoyin kula da lafiya matakin farko, yayin da aka shigar da ma’aikatan GAVI cikin tsarin albashin jihar.

Haka kuma, ya ce gwamnatin ta gina hanyoyi, ta samar da bas-bas da tallafin sufuri, tare da rabon hatsi da kayan noma ga ma’aikata a duk shekara.

A fannin ilimi kuwa, Usman ya ce an gyara makarantun sakandare 320, an gina sabbin ƙananan sakandare 30 da manyan sakandare 18.

Ya ce an kuma samar da kwamfutoci sama da 2,000 ga makarantu 100, tare da aiwatar da sabon tsarin mafi ƙarancin albashi ga ma’aikatan Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kebbi da ke Aliero da kuma Kwalejin Kimiyya ta Jihar Kebbi.

Sai dai shugaban NLC ya amince da cewa har yanzu akwai ƙalubalen da ke fuskantar ma’aikata, musamman hauhawar farashin kayayyaki, raguwar ƙarfin saye, ƙarin girma, alawus-alawus da ci gaban aiki.

Da yake magana kan alkawarin Malami na biyan mafi ƙarancin albashi na N110,000 idan aka zaɓe shi a shekarar 2027, Usman ya ce ya kamata a auna irin wannan alkawari bisa ƙarfin kuɗin gwamnati, hanyoyin samun kuɗaɗe, dorewa da kuma tsarin aiwatar da shi.

Advertisement

Ya ce bayyana adadi mai yawa a lokacin yaƙin neman zaɓe abu ne mai sauƙi, amma tabbatar da dorewar abin da aka yi alkawari shi ne babban ƙalubale.

Usman ya jaddada cewa NLC ƙungiya ce mai zaman kanta, wadda ba ta nuna goyon baya ga kowace jam’iyyar siyasa.

Ya ce ƙungiyar za ta ci gaba da yaba wa gwamnati idan ta yi abin da ya dace, ta nemi gyara inda ake buƙata, sannan ta yi adawa da duk wani mataki da zai tauye haƙƙin ma’aikata.

Ya yi kira ga ’yan siyasa da su gina kamfen ɗinsu kan gaskiya da manufofin da za su iya aiwatarwa, maimakon amfani da batun jin daɗin ma’aikata wajen neman ƙuri’a.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending