News
2027: INEC Za Ta Bayyana Matsayarta Kan Takarar Pantami, Nami, Adamu A Yau
Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) na shirin bayyana matsayarta kan halaccin wasu ’yan takara a zaben 2027, bayan hukuncin da Kotun Koli ta yanke kan wasu tanade-tanaden Dokar Zabe da suka shafi gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyu.
Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, zai gudanar da taron manema labarai a yau Talata, inda ake sa ran zai yi karin haske kan matsayin hukumar da kuma makomar wasu ’yan takarar da hukuncin Kotun Koli ya shafa.
Shugaba Tinubu Ya Ayyana Makokin Kwana Uku Kan Hatsarin Jirgin Sojoji A Ondo
Kotun Koli ta tabbatar da ingancin sassa na 77 da 84 na Dokar Zabe ta 2026, wadanda suka tanadi cewa jam’iyyu su mika wa INEC rajistar mambobinsu kafin gudanar da zaben fidda gwani.
Dokar ta kuma tanadi cewa mambobin da ba su cikin rajistar da aka mika wa hukumar ba, ba za su samu damar kada kuri’a ko neman takara a zaben fidda gwani ba.
A Jihar Gombe, ana ci gaba da nuna damuwa kan makomar tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami, wanda ya fice daga jam’iyyar APC zuwa PDP bayan ya janye daga takarar gwamnan jihar a karkashin APC.
Sai dai wasu jagororin PDP sun ce hukuncin Kotun Koli bai tabbatar da cewa Pantami ba ya cikin rajistar mambobin PDP da aka mika wa INEC ba. Sun kuma yi nuni da cewa jam’iyyar ta gudanar da wani sabon zaben fidda gwani bayan da kotu ta soke na farko.
A Jihar Neja kuwa, ana tambayar sahihancin takarar dan takarar PDP na gwamna, Muhammad Nami, sakamakon zargin cewa ya kasance dan takarar sanata a karkashin APC kafin daga bisani ya koma PDP.
Wani lauya mai kula da harkokin kundin tsarin mulki, Abdulmumin Jibril Abdullahi, ya ce takarar Nami na iya fuskantar kalubalen shari’a idan aka tabbatar da cewa ba a saka sunansa cikin rajistar mambobin PDP da aka mika wa INEC cikin wa’adin da doka ta tanada ba.
Haka kuma, hukuncin Kotun Koli ya haifar da tambayoyi kan takarar tsohon Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Mohammed Abubakar Adamu, a Nasarawa, wanda ya maye gurbin dan takarar SDP bayan ya janye daga takarar.
Sai dai magoya bayan tsohon IGP sun ce tsarin da ya kai shi takara ya bi ka’idojin doka, suna mai cewa shi ba shi ne wanda ya shigar da karar da Kotun Koli ta yanke hukunci a kanta ba.
A karkashin Sashe na 77 na Dokar Zabe ta 2026, wajibi ne jam’iyyu su mika wa INEC rajistar mambobinsu akalla kwanaki 21 kafin gudanar da zaben fidda gwani.
Dokar ta kuma hana jam’iyyu amfani da wata rajistar daban wajen gudanar da zaben fidda gwani, lamarin da ya sanya hukuncin Kotun Koli ya zama muhimmin batu ga jam’iyyu da ’yan takarar da ke shirin shiga zaben 2027.
