Connect with us

News

An Kama Matashi Kan Zargin Kashe Abokinsa Kan N500 A Jigawa

Published

on

Yan sanda sun cafke wani ango a ranar ɗaurin aurensa kan zargin kisan kai

Rundunar ƴan sandan Jihar Jigawa ta kama wani matashi mai shekaru 20, Lawisi Safiyanu, bisa zargin kashe abokinsa, Muhammad Abba, mai shekaru 25, kan bashin Naira 500.

An ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12:30 na daren 1 ga Oktoba, 2026, a Ƙauyen Chamo da ke Dutse.

Allah Ya Yi Wa Kakakin Hukumar Kashe Gobara Ta Jihar Kano, CFO Saminu Yusuf Abdullahi, Rasuwa

Kakakin rundunar, SP Lawan Shiisu Adam, ya ce binciken farko ya nuna cewa Muhammad ya sayi waya kan Naira 1,500, inda ya biya Naira 1,000, ya rage bashin Naira 500.

Ya ce rashin biyan sauran kuɗin ne ya jawo takaddama tsakanin mutanen biyu, inda ake zargin Lawisi ya daba wa Muhammad wuƙa.

A cewarsa, an garzaya da Muhammad zuwa Asibitin Rashid Shekoni da ke Dutse domin samun kulawa, amma daga bisani ya rasu sakamakon raunin da ya samu.

Advertisement

SP Lawan ya ce ƴan sandan sun kama wanda ake zargin tare da kwato wuƙar da ake zargin an yi amfani da ita wajen aikata laifin.

Ya ƙara da cewa an kammala binciken farko kuma an gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu domin fuskantar shari’a.

Kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Tijjani Murtala, ya gargadi jama’a da su guji ɗaukar doka a hannunsu, yana mai kira gare su da su kai rahoton duk wata takaddama ko rikici ga hukumomin tsaro.

Kwamishinan ya tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da ƙoƙarin cafke masu aikata laifuka tare da gurfanar da su a gaban kotu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending