News
Ƴan Bindiga Sun Hallaka Mutane 17 A Zamfara
’Yan bindiga sun kashe akalla mutane 17 a wasu hare-hare da suka kai wani wurin haƙar zinare da kuma wani ƙauye a ƙaramar hukumar Maru ta Jihar Zamfara.
Rahotanni sun ce maharan ɗauke da makamai, waɗanda ke kan babura, sun kai harin ne a ranar Litinin a wani wurin haƙar ma’adinai da ke wajen ƙauyen Bindin.
Kwamishinan Ƴansandan Kano Ya Bukaci Sarki Aminu Ado Ya Janye Shirin Sa Na Hawan Fatahu Yakasai
A cewar hukumomin yankin, maharan sun fara kai hari kan masu haƙar zinare, inda suka harbe mutane biyar har lahira.
Daga bisani, maharan sun shiga ƙauyen, inda suka yi arangama da jami’an tsaro. A yayin arangamar ne aka kashe wasu mutane 12, lamarin da ya ɗaga adadin waɗanda suka rasa rayukansu zuwa 17.
Mai ba da shawara kan harkokin ƙauyen, Abdullahi Musa Mutunji, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa harin na iya kasancewa ramuwar gayya ne.
Ya ce wasu masu haƙar ma’adinai sun kashe wani ɗan bindiga da ya yi musu barazana, wanda hakan ya jawo harin.
