Connect with us

News

Gwamnatin Kebbi Ta Amince Da Biyan N75,000 A Matsayin Karin Albashi Ga Malamai 17,620

Published

on

IMG 20261008 WA0000

Daga Khadijat Saidu,Birnin Kebbi.

Gwamnatin Jihar Kebbi ta amince da biyan mafi karancin albashi na Naira 75,000 ga malamai 17,620 a fadin jihar, wanda hakan ya daidaita albashinsu da na sauran ma’aikatan gwamnati.

Da yake jawabi ga manema labarai a Birnin Kebbi a ranar Laraba, Shugaban Kungiyar Malaman Najeriya (NUT) na Jihar Kebbi, Kwamared Abubakar Zaki, ya yaba wa Gwamna Nasir Idris bisa cika alkawarin da ya yi na inganta walwalar malamai.

Jami’an Ƴansanda Sun Kama Wani Mutum Kan Zargin Kona Gidan Yayansa A Jigawa 

Ya ce amincewar ta biyo bayan sahalewar da Gwamna Nasir Idris ya yi wa farar takarda (White Paper) kan rahoton da kwamitin da aka kafa domin tantance malamai a jihar ya mika.

A cewarsa, an kafa kwamitin ne domin tantance adadin sahihin malamai da wadanda ba sahihi ba, da kuma duba tsarin albashinsu da kuma tabbatar da ainihin adadin malamai a jihar.

Advertisement

Zaki ya bayyana Gwamna Idris, wanda shi kwararren malami ne kuma tsohon shugaban kwadago, a matsayin shugaban da ya nuna jajircewa wajen inganta walwalar malamai da fannin ilimi.

“A matsayinsa na kwararren malami kuma tsohon shugaban kwadago, Gwamna Idris ya nuna kishin kasa da tausayi wajen daga darajar malamai, sana’ar koyarwa da kuma fannin ilimi,” in ji shi.

A cewarsa, kungiyar ta kuma yaba da irin jarin da gwamnatin ta zuba wajen gyaran makarantu 2,650 da kuma gina sabbin makarantu 200 domin samar da yanayi mai kyau na koyo da koyarwa.

Ya bayyana cewa bayan tantancewar da gwamnan ya bayar da umarni da kuma amincewa da sabon albashin a watan Satumba, malamai za su fara cin gajiyar sabon tsarin albashi daga watan Oktoba.

“Bayan aikin tantancewa da Gwamnan ya bayar da umarni da kuma amincewa da mafi karancin albashi na N75,000 a watan Satumba, malamai a Kebbi za su fara cin gajiyar sabon tsarin albashi daga wannan watan na Oktoba,” in ji Zaki.

Ya kara da cewa Gwamna Idris a baya ya tsawaita shekarun ritaya ga malamai daga shekaru 60 zuwa 65 da kuma shekarun aiki daga 35 zuwa 40, wani sauyi da ya dade yana fafutuka a kai a lokacin da yake Shugaban NUT na kasa.

Advertisement

Shugaban NUT din ya yi kira ga malamai da su mayar da martani ga wannan karamci na gwamnati ta hanyar kara jajircewa, himma da kuma kwarewa a aikinsu.

Ya yi karin haske cewa mafi karancin cancanta ta shiga aikin koyarwa a jihar ita ce takardar NCE ko Diploma, duk da cewa malamai da dama na da digiri na jami’a da HND, tare da ci gaba a matakin aiki daga Grade Level 07 zuwa Grade Level 15 da 16.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending